Buhari ya gaza, ka rabu da shi ka dawo PRP - Balarabe Musa ya shawarci fitaccen Sanatan Arewa

Buhari ya gaza, ka rabu da shi ka dawo PRP - Balarabe Musa ya shawarci fitaccen Sanatan Arewa

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Alhaji Balarabe Musa yace Sanata Shehu Sani da sauran Sanatocin jam'iyyar APC suna da ikon ficewa daga jam'iyyar APC su koma wasu jam'iyyun saboda gazawar gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari.

A hirar da Balarabe Musa ya yi da Guardian a jiya, yace, "Ni ban bawa Shehu Sani shawarar ya cigaba da kasancewa a jam'iyyar APC ba, yanzun abinda ya fito karara cewa abinda ya samu jam'iyyar PDP a shekarar 2015 lokacin da suka gaza cika alkawurran da suka yiwa al'umma shi ke faruwa da APC.

Idan har Shehu Sani ya fice daga jam'iyyar APC, ina bashi shawara ya dawo jam'iyyar People's Redemption Party (PRP) inda tun farko yake da tushe da asali".

Buhari ya gaza, Ka rabu da shi ka dawo PRP - Balarabe Musa ya shawarci fitaccen Sanatan Arewa

Buhari ya gaza, Ka rabu da shi ka dawo PRP - Balarabe Musa ya shawarci fitaccen Sanatan Arewa

DUBA WANNAN: Kasashe 10 da suka fi talauci a nahiyar Afirka

"Gwamnatin ta gaza tabuka wa al'umma ayyukan da suka dace, hakan yaza mambobin jam'iyyar ke ficewa. Ina tsamanin yawancin su zasu koma jam'iyyun adawa saboda su ceto kasar nan daga mawuyacin halin data fada.

Bana tsamanin APC zata cigaba da kasancewa kan karagar mulki bayan shekarar 2019, kamar yadda aka hambarar da PDP daga mulki a shekarar 2015. Ina tsamanin mutane da yawa zasu cigaba da ficewa daga APC".

A bangarensa, mai bawa Shehu Sani shawara kan siyasa da tsare-tsare, Suleiman Ahmed, yace akwai manyan mutane da dama da suka shawarci Sanata Shehu Sani ya cigaba da kasancewa a jam'iyyar APC.

A cewarsa, Shugaba Buhari, Shugaban APC, Adams Oshiomhole da Bola Tinubu suna daga cikin shugabanin jam'iyyar da suka shawarci Sani kada ya fice daga jam'iyyar APC, inda su kayi alkawarin cewa za'a magance matsalolin da suka taso a jam'iyyar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel