'Abin da yasa Nasir El-Rufai ke fushi da Bukola Saraki'

'Abin da yasa Nasir El-Rufai ke fushi da Bukola Saraki'

- Gwamnan jahar Kaduna yana fushi da Shugaban majalisa

- A shekarar data gabata ne gwamnan ya nemi a bawa jahar sa rancen kudi

- Shehu Sani shiya bada shawarar kar a bawa jahar Kaduna bashin

'Abin da yasa Nasir El-Rufai ke fushi da Bukola Saraki'

'Abin da yasa Nasir El-Rufai ke fushi da Bukola Saraki'

Wani mai kafa doka Rafiu Ibrahim (PDP, Kwara) yace gwamnan jahar Kaduna Nasir El rufa'i yana fushi da Shugaban majalisa Bukola Saraki saboda sanatan yaki amincewa da rancen $350 da jahar ta nema.

A shekarar data gabata ne jahar ta nemi da a bata rancen kudin.

El-rufa'i yace jahar tana bukatar kudin ne don yiwa jahar wasu aikace aikace.

A watan Mayu ne sanatan yaki amincewa da bada bashin biyo bayan wani kwamiti daya kafa a karkashin jahorancin Shehu Sani inda ya soki bashin da jahar ta nema.

DUBA WANNAN: An sake kashe dan Najeriya a Afirka ta Kudu

Akwai yar tsama a tsakanin El rufa'i da Shehu Sani tun a shekarar 2015.

Shugaban majalisar ya shawarci gwamnan daya zauna su tattauna da sanatoci Uku dake jahar domin su goya masa baya a majalisa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel