An kuma bindige wanii dan Najeriyar a Afirka ta Kudu, abin yaki karewa

An kuma bindige wanii dan Najeriyar a Afirka ta Kudu, abin yaki karewa

- Al'ummar Najeriya mazauna kasar South Africa sun tabbatar da kashe Chibuzo Nwankwo, Dan shekaru 42, dan asalin jihar Enugu

- Kisan Nwankwo shine na 121 a jerin yan Najeriya da ake kashe a South Africa tun daga watan janairu na 2016

- Habib Miller, sakataren watsa labarai na kungiyar yan Najeriya daka South Africa ya tabbatar wa da ofishin dillancin labarai a ranar asabar

An kuma bindige wanii dan Najeriyar a Afirka ta Kudu, abin yaki karewa

An kuma bindige wanii dan Najeriyar a Afirka ta Kudu, abin yaki karewa

Al'ummar Najeriya mazauna kasar South Africa sun tabbatar da kashe Chibuzo Nwankwo, Dan shekaru 42, dan asalin jihar Enugu.

Kisan Nwankwo shine na 121 a jerin yan Najeriya da ake kashe a South Africa tun daga watan janairu na 2016.

Habib Miller, sakataren watsa labarai na kungiyar yan Najeriya daka South Africa ya tabbatar wa da ofishin dillancin labarai a ranar asabar.

Kamar yanda yace, an kashe Nwankwo ne a safiyar juma'a a wata mashaya dake Kempton Park, Johannesburg, bayan yar hayaniya da wani mutum da ba a sani ba.

"Mamacin, wanda ya saba zuwa mashayar, ya bugu sai ya fara damun wata ma'aikaciyar mashayar.

"Labarin da kungiyar ta samu, masu tsaron mashayar suka Koro Nwankwo daga ciki amma ya cigaba da komawa, har dai ya fusata kafin aika aikar ta faru "

DUBA WANNAN: Miyetti Allah ga Gowon, Kai ma ka san mu ba muggai bane

Mista Miller yace daga baya yan sandan kasar sun shiga al'amarin inda suka kama wanda yayi kisar.

"An kama shi da laifin Kisan kai kuma ana ta bincike, muna rokon yan Najeriya dasu kwantar da hankalin su kuma su bar doka tayi aikin ta" inji Mista Miller

Yace kungiyar su zata cigaba da bibiyar yan sandan har sai sun tabbatar anyi adalci.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel