2019: A matse APC take, komai ma tana iya fadi don ta zarce - r-APC

2019: A matse APC take, komai ma tana iya fadi don ta zarce - r-APC

- Har yanzu ba'a samu damar dunke barakar cikin gidan APC ba

- Barakar ta bada damar a kwace majalisa nan gaba ta koma PDP

- Babu kamshin gaskiya kan batun su waye masu rinjaye tsakanin PDP da APC

2019: A matse APC take, komai ma tana iya fadi don ta zarce - r-APC

2019: A matse APC take, komai ma tana iya fadi don ta zarce - r-APC
Source: Twitter

Kakakin sabuwar jam'iyya watau R-APC wadda Buba Galadima ke shugabanta, Kassim Afegbua, ya zanta da manema labarai, inda yace akwai rina a kaba ganin yadda APC ke kokarin shafa musu kashin kaji, inda yace ai a matse suke.

A cewarsa, kashe-kashe da ke ta karuwa a jihohi da manyan tituna, kasawar shugaba Buhari ce ta janyo su, kuma babu wani katabus da gwamnatin keyi a halin yanzu sai alkawurran bogi.

DUBA WANNAN: Martanin Miyetti Allah ga Gowon

A ganin Mista Afegbua dai, matsuwa ce ta kai har ake jiyo gwamnati na daukar sabbin alkawurra duk da cewa ta kasa cika na baya da ta dauko wa talakawa.

Adams Oshiomhole dai, yace yan tawayen dama basu da katabus koa sanda suna APCn, bayan duk kokarinsa na kar su balle yaci tura.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel