Babu wanda zai koma APC cikin mu - Sanata Hunkuyi

Babu wanda zai koma APC cikin mu - Sanata Hunkuyi

Sanata Suleiman Hunkuyi, mai wakiltan Kaduna ta Arewa ya yi alkawarin taimakawa jam'iyyar PDP kwace mulki daga hannun APC a zaben shekarar 2019 a jihar.

Hukunyi yana daya daga cikin Sanatoci 14 da suka sauya sheka daga jam'iyyar APC zuwa wasu jam'iyyun a ranar Talata 19 ga watan Yulin wannan shekarar.

Hukunyi ya kuma jadada cewa babu abinda zai sa su koma jam'iyyar APC.

Sanatan ya yi wannan furucin ne yayin da ya kai ziyara a Sakatariyar PDP dake Kaduna a ranar Juma'a, yace ya yanke hukuncin komawa PDP ne saboda yarjejenyar da su kayi tsakanin shugabanin R-APC da PDP.

Karyar Sanata Lawal da yawa take, babu wanda zai koma APC cikin mu - Hunkuyi

Karyar Sanata Lawal da yawa take, babu wanda zai koma APC cikin mu - Hunkuyi
Source: Instagram

DUBA WANNAN: An yiwa manya-manyan sojojin Najeriya canjin ayyuka

"Mun zo mu fada muku cewa mun fice daga APC kuma mun shigo PDP kuma babu abinda zai sa mu koma APC.

"Mun shigo PDP ne kwanmu da kwarkwata tare da dukkan magoya bayanmu don mu hada hannu da karfe wajen kwace mulki daga jam'iyyar APC a jihar Kaduna," a cewar Hunkunyi.

Ya yi kira ga shugabanin PDP su hada kai da wadanda suka shigo jam'iyyar don kayar da gwamnatin APC a zaben na shekarar 2019.

Hunkuyi ya kuma bukaci shugaban PDP na jihar Kaduna, Feli Hyat, ya kafa wata kwamiti wanda dauke da mambobin da suka sauya sheka da sauran 'yan jam'iyyar don kafar ranar da za'ayi maraba da wanda suka shigo jam'iyyar.

A cewarsa, siyasa sai da mutane ake yinta, hakan yasa Hukunyi ya yi alkawarin zai shawo kan dukkan magoya bayansa su koma PDP kafin babban zaben shekarar 2019.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ta ruwaito cewa Hunkuyi ya ziyarci sakatariyar PDP ne tare da 'yan majalisar wakilai biyu; Lawal Rabiu da Rufai Chanchangi.

A bangarensa, Mr Hyat ya yi alkawarin jam'iyyar PDP tana maraba da sabbin zuwan kuma za suyi aiki tare babu nuna bananci don ganin sunyi nasara a 2019.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel