Sanata Hunkuyi ya bayar da Hakuri na barin jam'iyyar PDP a 2015

Sanata Hunkuyi ya bayar da Hakuri na barin jam'iyyar PDP a 2015

Sanata mai wakilicin mazabar jihar Kaduna ta Arewa a majalisar dattawa, Sanata Suleiman Hunkuyi, ya bayar da hakuri tare da neman yafiya ta sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa jam'iyyar APC a shekarar 2015 da ta gabata.

Hukunyi kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwiato, ya bayyana hakan ne yayin ganawa da masu ruwa da tsaki na jam'iyyar PDP a ofishin ta dake kan hanyar Unguwar Kanawa ta jihar Kaduna a ranar Juma'ar da ta gabata.

Sanata Hunkuyi ya bayar da Hakuri na barin jam'iyyar PDP a 2015

Sanata Hunkuyi ya bayar da Hakuri na barin jam'iyyar PDP a 2015

A yayin gabatar da jawaban sa ga maza da mata na jam'iyyar, Hunkunyi, wanda a kwana-kwanan nan Ungulu ta koma gidan ta na tsamiya watau jam'iyyar PDP, ya sha alwashin fatattakar gwamnan jihar, Mallam Nasir El- Rufa'i daga kujerar sa a zaben 2019.

KARANTA KUMA: Wasu 'Yan sanda sun yi kuskuren harbe wani jami'in SARS har Lahira a jihar Anambra

Legit.ng ta fahimci cewa, a ranar Larabar da ta gabata Hunkuyi na daya daga cikin Sanatoci 14 da aka yi shellar sauyin shekar su daga jam'iyyar APC a farfajiyar majalisar dattawa.

Hunkuyi ya nemi afuwa tare da bayar da hakurin sa sakamakon ficewa daga jam'iyyar PDP yayin da guguwar zaben 2015 ta kada, tare da taimakon El-Rufa'i wajen lashe kujerar gwamnatin jihar ta Kaduna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel