Ko daga 'gadon asibiti' Buhari zai lashe zabe a jihohin Bauchi, Sokoto da Kano - Ministan Buhari

Ko daga 'gadon asibiti' Buhari zai lashe zabe a jihohin Bauchi, Sokoto da Kano - Ministan Buhari

A jiya Juma'a, Ministan Sufuri na Najeriya, Mr. Rotimi Amaechi, ya yi ikirarin cewa gwamnonin jihohin Kwara da Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal da Abdulfatah Ahmed za su fice daga jam'iyyar APC.

Ministan yace Tambuwal zai fice ne saboda yana son fitowa takarar shugabancin kasa kuma yasan ba zai samu tikiti a jam'iyyar APC ba.

Mr. Amaechi, ya kuma ce shugaba Muhammadu Buhari zai lashe zabe a jihohin Sakkwato, Kano da Bauchi a babban zaben shekarar 2019 ko da a 'gadon asibiti' aka tafi da shugaban kasar jihohin.

Buhari zai lashe zabe a Sakkwato, Kano da Bauchi ko da yana kwance ne - Amaechi

Buhari zai lashe zabe a Sakkwato, Kano da Bauchi ko da yana kwance ne - Amaechi

Ministan yace shaidawa manema labarai cewa baya son yin tsokaci kan lamuran siyasa, sai dai yace duk da sauyin shekar da wasu 'yan jami'yyar APC a majlisar tarayya su kayi, jam'iyyar APC ce zata lashe zaben 2019.

DUBA WANNAN: Ana yinta: Ganduje ya shiga zawarcin Shekarau zuwa APC a Kano

A lokacin da manema labaran suke ce masa akwai yiwuwar APC zata ruguje saboda yadda mutane ke fice daga jam'iyyar, Ministan ya kada baki yace, "Wannan ra'ayin ku ne, kuma ku ba 'yan siyasa bane saboda haka ba zaku iya tsokaci kan abinda baku da masaniya a kanta ba. Duk da bani son magana kan siyasa, sai da kuka tursasa ni nayi tsokaci.

"Maganan gaskiya shine, Gwamnan jihar Sakkwato zai fice daga APC da kansa. Yana son fitowa takarar shugabancin kasa. Haka shima gwamnan Kwara, mutanen nan dukkansu muna tsamanin zasu fice."

"Ko da a gadon asbiti ka kai Buhari jihohin Bauchi da Kano, zai yi nasara a zaben saboda bai taba fadi zabe a Bauchi ba. Sai dai hakan ba zai sa mu tankware hannu muna kalo ba domin abokan hamayya na iya bamu mamaki."

Amaechi ya kuma ce jinkirta fidda dan takarar shugaban kasa da jam'iyyar adawa tayi abin alkhairi ne ga jam'iyyar APC.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel