Allah ya yiwa shahrarren dan kwallo, Ahmed Musa, karuwa

Allah ya yiwa shahrarren dan kwallo, Ahmed Musa, karuwa

- Allah ya yiwa Shahrarren dan wasan kwallon kafar Najeriya kuma, Ahmed Musa, karuwa.

- Allah ya azurta dan kwallon da uwargidarsa, Juliet Ejue, da ‘da namiji.

A jiya Alhamis, 26 ga watan Yuli 2018 ne Allah ya azurta shararen dan kwallon Najeriya kuma dan jihar Kano, Ahmed Musa da 'da namiji.

Dan kwallon ya alanta wannan albishir a shafin sada ra’ayi da zumuntarsa tare da sanya hoton dan jaririn.

Yace: "Ina son sanar da ku cewa Allah ya albarkaceni da ‘da namiji! Ina matukar farin ciki".

KU KARANTA: ‘Dan Majalisar APC ya nemi a biya sa kudi ya koma PDP

Shekara daya da watanni biyu kenan da Ahmed Musa ya sake aure bayan rabuwarsa da matarshi ta farko, Jamila, a kasar Ingila. Ya rabu da ita ne bayan wani rahoto ya bayyana cewa da kwallon ya bugi matarsa. Jamila ta haifa masa yara biyu kafin rabuwarsu.

Ahmed Musa ya auri Juliet Ejue, yar asalin jihar Kross Riba a ranan 14 ga watan Mayun 2017.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel