Yadda Tinubu, Oshiomole da Balarabe Musa suka hana ni sauya sheka – Shehu Sani

Yadda Tinubu, Oshiomole da Balarabe Musa suka hana ni sauya sheka – Shehu Sani

Daga baya-bayan nan labarai sun fara bayyana kan yadda shugaban jam’iyyar APC, Adams Oshiomole; babban jigo a jam’iyyar, Bola Tinubu, da shugaban jam’iyyar PRP, Balarabe Musa, suka hana sanata Shehu Sani sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP.

Shehu Sani ya kasance daya daga cikin masu kukan zaluncin da ake musu a jam’iyyar kuma ya kudirta niyyar fita daga jam’iyyar.

A ranan Talata, 15 daga cikin sanatocin jam’iyyar APC suka sauya sheka daga jam’iyyar, 12 suka koma jam’iyyar adawa ta PDP.

Yadda Tinubu, Oshiomole da Balarabe Musa suka hana ni sauya sheka – Shehu Sani

Yadda Tinubu, Oshiomole da Balarabe Musa suka hana ni sauya sheka – Shehu Sani

Yayinda yake magana da jaridar Premiuim Times, Shehu Sani ya bayyana cewa sa bakin wasu jigogin jam’iyyar da ya canza aniyarsa.

Yace: “Asiwaju Tinubu, Oshiomole da Balarabe Musa ne suka hana ni sauya sheka. Da farko sun tabbatar da cewa an zalunceni a jiha Kaduna.

“Balarabe Musa ya gayyaceni gidansa, ya gargadeni kuma ya bani shawara kada in sauya sheka. Hakazalika Asiwaju. Adam Oshiomole ya tunatar da ni yakin gwagwarmayan da nayi.”

“Sun jawo hankalina kan cewa dukkan wadanda suka koma PDP, anguluce ta koma gidanta na tsamiya. Ni kuma bani da hali irin nay an PDP. Ni dan gwagwarmaya ne.”

“Sun bani tabbacin cewa za’a shawo kan komai. Sun tabbatar mini da cewa za su sanya baki cikin wannan al’amari. Shi yasa na kasa sauya sheka.”

KU KARANTA: ‘Dan Majalisar APC ya nemi a biya sa kudi ya koma PDP

Bayan wadannan mutane uku da suka bashi shawara, Shehu Sani ya kara da cewa sa bakin Femi Falana, malaman addini da yan mazabarsa ne suka canza masa rai.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel