Ekweremadu ya isa jihar Enugu, ya yi tir da kashe-kashe a Kasar nan

Ekweremadu ya isa jihar Enugu, ya yi tir da kashe-kashe a Kasar nan

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu, ya bayyana takaicin sa dangane da kashe-kashe da zubar da jini dake faman aukuwa a kasar nan, inda yake neman a zauna lafiya domin al'umma su ci gaba da gudanar da harkokin su cikin kwanciyar hankali da nutsuwa.

Ekweremadu ya bayyana hakan ne a ranar Juma'ar da ta gabata yayin da dubunnan magoya baya suka yi lalare maraba da zuwan sa jihar Enugu.

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya ruwaito, Mataimakin shugaban majalisar ya isa Mahaifar ta sa ne bayan da wasu jami'an tsaro suka yiwa gidan sa dake birnin Abuja kawanya tare da hana shige da fice a ranar Talatar da ta gabata.

Ekweremadu ya isa jihar Enugu, ya yi tir da kashe-kashe a Kasar nan

Ekweremadu ya isa jihar Enugu, ya yi tir da kashe-kashe a Kasar nan

Sanatan ya bayyana takaicin sa dangane da yadda ake ci gaba da rasa rayukan mutane cikin sassa da dama na kasar nan. Ya kuma bayyana sha'awar sa kan yadda yanayi zai kasance al'ummar kasar nan su ci ga da gudanar da harkokin su cikin sukuni.

KARANTA KUMA: Fadar Shugaban 'Kasa ta roƙi Majalisar Tarayya kan amincewa da buƙatar Buhari ta kasafin zaben 2019

Legit.ng ta fahimci cewa Sanatan mai wakilcin Enugu ta Yamma a majalisar dattawa, ya kuma bayyana damuwar sa dangane da yadda ake yiwa dokokin kasar nan karan tsaye da hakan ke janyo barazanar zagon kasa ga dimokuradiyya.

Dan majalisar ya kuma yi godiya tare da yabawa magoyan bayan sa dangane da wanna soyayya gami da kauna da suke ci gaba da nunawa a gare sa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel