Ana yinta: Ganduje ya shiga zawarcin Shekarau zuwa APC a Kano

Ana yinta: Ganduje ya shiga zawarcin Shekarau zuwa APC a Kano

Rahottanin da muka samu daga Daily Trust sun bayyana cewa Gwamna Umar Abdullahi na jihar Kano yana zawarcin tsohon Gwamna Ibrahim Shekarau zuwa jam'iyyar na APC gabanin zaben shekarar 2019.

Wata kwakwarar majiya na kusa da Shekarau ta sanar da Daily Trust a jiya cewa wasu kusoshin jam'iiyyar APC a Kano da Abuja sun tattauna da Shekarau da mutanensa inda suke kokarin shawo kansu su dawo jam'iyyar APC da aka kafa tare dasu tun farko.

Majiyar tace an tsananta zawarcin ne cikin kwanakin nan bayan ficewar tsohon gwamna kuma dan majilisa a jihar, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso da ya fice daga APC zuwa PDP a ranar Talata.

Ana yinta: Ganduje ya shiga zawarcin Shekarau zuwa APC a Kano

Ana yinta: Ganduje ya shiga zawarcin Shekarau zuwa APC a Kano

Kwankwaso dai tuni run raba jihar da Ganduje kuma majiyar tace gwamna Ganduje na kokarin hada karfi da karfe ne tare da Shekarau domin tabbatar da cewan an sami nasara a babban zaben shekarar 2018 mai zuwa.

DUBA WANNAN: Kotu ta tsige wani basarake a dan gatan gwamnan jihar Adamawa

Wata majiyar daban kuma tace Gwamna Ganduje ya gana da wasu na kusa ga Shekarau a babban birnin tarayya Abuja.

"Cikin wadanda aka gana dasu har da tsaffin kwamishinoni da masu bayar da shawara na musamman da su kayi aiki karkashin Shekarau a lokacin da yake gwamna a jihar Kano.

"Ina tabbatar muku cewa ana son Shekarau ya bayar da dan takara da zai maye gurbin mataimakin gwamnan jihar Kano, Farfesa Hafiz Abubakar wanda za'a bukaci ya yi murabus nan gaba.

"Za'a bukaci ya yi murabus cikin lami-lafiya ko kuma a tunbuke shi da karfi a majalisar jihar Kano," inji majiyar.

A yayin da yake tsokaci kan batun, wani dan gani-kashenin Shekarau, Alhaji Muhammadu Inuwa Yusuf, yace yana maraba da hadin gwiwar don zata kara kawo cigaba a Kano da kasa baki daya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel