Kakar su zata yanke saka: Buhari zai duba bukatar yankin Naija-Delta a kan rabon arzikin kasa

Kakar su zata yanke saka: Buhari zai duba bukatar yankin Naija-Delta a kan rabon arzikin kasa

Shugaba Muhammadu Buhari yace gwamnatinsa zata duba batun ware wa yankin Naija-Delta 13% cikin kudaden da ake samu daga sayar da danyen man fetur domin samar da ayyukan more rayuwa da cigaba a yankin kamar yadda yake cikin kundin tsarin mulki.

Shugaban kasan ya bayar da wannan tabbacin ne a yau Juma'a yayin da ya karbi bakuncin masu sarautun gargajiya na yankin tare da wasu manyan mutane daga Isolo Delta a karkashin jagorancin Ovrawah Omogha 1, Odiologbo na Oleh a fadar shugaban kasar dake Abuja.

Shugaba Buhari ya shaida musu cewa gwamnatinsa zata yi nazarin abubuwan da kundin tsarin mulki ya tanadar wa yankin musamman abinda ya danganta ayyukan gwamnatin tarayya a yankunan.

Kakar su zata yanke saka: Buhari zai duba bukatar yankin Naija-Delta a kan rabon arzikin kasa

Kakar su zata yanke saka: Buhari zai duba bukatar yankin Naija-Delta a kan rabon arzikin kasa

DUBA WANNAN: Babu wanda zamu bawa tikiti hannu-daya babu zaben cikin gida - Oshiomhole

"Na saurari koke-koken ku, zanyi nazarin kan irin cigada da ayyuka da akayi a yankin musamman a fannin man fetur, iskar gas da gine-gine.

"Zan duba batun bawa yankin 13% cikin kudaden danyen man fetur don ganin abinda gwamnatocin baya su kayi, saboda mu san abinda gwamnati na zata iya yi game da bukatar," inji shugaban kasan.

Shugaban kasan ya kuma lura cewa mutanen yankin Isolo sun kasance masu fasaha ne da kwazo wajen sana'o'i daban-daban.

Ya kuma yi alkawarin ganin cewa an yiwa yankin Isolo adalci wajen rabon arzikin kasa.

A jawabinsa, Shugaban kungiyar 'yan Isolo kuma mai magana da yawun masu sarautun gargajiyan, Iduh Amadhe, ya yabawa shugaba Muhammadu Buhari kan irin cigaban da ya samu.

Ya kuma roki shugaban kasan ya yi duba cikin harkokin yankin Naija-Delta domin samar musu ababen more rayuwa da cigaba.

Mr Amadhe yace babu wata takamamen aikin cigaba da aka yiwa yankin tun bayan kafa hukumar harkokin Naija-Delta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel