Wasu 'Yan sanda sun yi kuskuren harbe wani jami'in SARS har Lahira a jihar Anambra

Wasu 'Yan sanda sun yi kuskuren harbe wani jami'in SARS har Lahira a jihar Anambra

Wasu jami'an tsaro na 'yan sanda dake aikin gadi a wani babban gida sun sheke wani jami'in SARS (Special Anti-Robbery Sqaud) a unguwar Alor dake yankin karamar hukumar Idemili ta Kudu a jihar Anambra.

Kamar yadda binciken manema labarai na jaridar The Punch ya bayyana, wannan lamari na tsautsayi ya afku ne a ranar Juma'a ta yau daura da gidan Ministan ayyuka da kwadago, Sanata Chris Ngige.

Wasu 'Yan sanda sun yi kuskuren harbe wani jami'in SARS har Lahira a jihar Anamba

Wasu 'Yan sanda sun yi kuskuren harbe wani jami'in SARS har Lahira a jihar Anamba

Wani jami'in dan sanda da ya bukaci a sakaya sunan sa ya bayyanawa manema labarai a birnin Awka cewa, jami'an 'yan sanda sun yi kuskuren harbe jami'in na SARS da shima aka sakaya sunan sa, inda suka dauka cewar abokin aikin na su dan ta'adda ne mai garkuwa da mutane.

KARANTA KUMA: Shugaba Buhari na ganawa da Sarakunan Gargajiya na Isoko a Fadar sa ta Aso Villa

Wani babban jami'in SARS na reshen Awkuzu, Sunday Okpe, ya tabbatar da aukuwar wannan tsautsayi yayin ganawa da manema labarai a wayar tarho, inda ya ce marigayin na daya daga cikin makarraban sa.

Daga wata majiya kuma ta hukumar 'yan sanda, ta bayyana cewa a halin yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike na sirrance tare titsiye jami'an da tsautsayi ya afkawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel