Ya sami tikitin zama gidan kaso bayan da ya damfari matar tsohon gwamna

Ya sami tikitin zama gidan kaso bayan da ya damfari matar tsohon gwamna

- Kotu ta gurfanar da wani dan kasuwa a gabanta bisa laifin damfarar matar tsohon gwamnan jahar Kwara

- Alkalin kotun ya bada umarnin a sakaya shi kafin a yanke abinda za'a biya na Belin sa

- Lauyar dake kare wanda ake zargin ta nemi kotu ta bata belinsa

Ya sami tikitin zama gidan kaso bayan da ya damfari matar tsohon gwamna

Ya sami tikitin zama gidan kaso bayan da ya damfari matar tsohon gwamna

Wata kotu dake zamanta a Legas ta gurfanar da wani dan kasuwaa gabanta bisa laifin damfarar matar tsohon gwamnan jahar Kwara Alhaja Kuburat Lawal kudi har kimanin Miliyan 8.5.

Hukumar SCIID dake Panti-Yaba Legas ta samu nasarar cafke wanda ake tuhumar.

A watan Yuli na 2002 wanda ake zargin suka siyarwa matar tsohon gwamnan Automatic Gas Oil (AGO) wanda na karya ne.

Daga bayane suka kasa cika alkawarin da suka dauka na yin jigilar man fetur sannan suka gagara maida mata da kudinta.

Bayan gurfanar su a gaban kotu lauyar wanda ake kara Mrs Adekoya ta nemi da a bata belinsa sannan tace wanda ake zargin bazai taba guduwa ba kasancewar akwai gudanarwar yan sanda a cikin lamarin.

DUBA WANNAN: 'An saki bayanan sirri ga PDP'

Ta kara da cewa wanda take karewar yana fama da karancin lafiya.

Alkalin kotun Justice Hassan ya bada umarnin a garkame shi a gidan kaso zuwa 1 ga watan Augusta kafin nan an fitar da takarar belin nasa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel