El-Rufai ya caccaki Saraki kan sauya shekar Sanatoci

El-Rufai ya caccaki Saraki kan sauya shekar Sanatoci

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya zargi shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki da ambatan sunayen wasu mambobin majalisar All Progressives Congress (APC) cikin wadanda suka sauya sheka zuwa Peoples Democratic Party (PDP) ba tare da yardarsu ba.

El-Rufai yayi ikirarin cewa wasu daga cikin Sanatocin da Saraki ya ambata sun fito daga baya sunce ba sauya sheka za su yi daga APC ba sannan kuma basu san dalilin da yasa aka sanya sunayensu cikin masu sauya shekar ba, jaridar The Cable ta ruwaito.

Gwamnan wadda yayi magana a wata hira da wasu tashoshin radiyo a Kaduna a ranar Alhamis,ya ce majalisar dattawa karkashin jagorancin Bukola Saraki shine mafi muni da Najeriya ta taba yi.

El-Rufai ya caccaki Saraki kan sauya shekar Sanatoci

El-Rufai ya caccaki Saraki kan sauya shekar Sanatoci

El-Rufai ya kuma daura laifin rashin kammala ayyukan da ake yi a jiharsa akan Sanata Shehu Sani, Suleiman Hunkuyi da kuma Danjuma Laah.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Okorocha ya sanya N20m akan wadanda suka kashe jigon APC a Imo

El-Rufai ya ce rashin amincewa da sanatocin suka yi wajen ciwo bashin dala miliyan 350 daga bankin duniya zuwa jihar shine ya haddasa rashin kammaluwan aikin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel