Yanzu Yanzu: Okorocha ya sanya N20m akan wadanda suka kashe jigon APC a Imo

Yanzu Yanzu: Okorocha ya sanya N20m akan wadanda suka kashe jigon APC a Imo

Gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha yayi alkawarin bayar da naira miliyan 20 ga duk mutumin da ya bayar da bayani mai amfani akan wadanda suka kashe jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar.

Gwamnan ya dauki wannan alkawari ne a ranar Juma’a, sa’o’i kadan bayan wasu yan bindiga sun kashe shugaban APC a karamar hukumar Ideato ta arewa, Mista Sunny Ejiagwu.

Yanzu Yanzu: Okorocha ya sanya N20m akan wadanda suka kashe jigon APC a Imo

Yanzu Yanzu: Okorocha ya sanya N20m akan wadanda suka kashe jigon APC a Imo

An kashe Mista Ejiagwu kwanaki hudu bayan an zabe shi a matsayin shugaban APC a karamar hukuma, a hanyarsa ta komawa gida bayan ya halarci taro a sakatariyar APC na Owerri, babban birnin jihar.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Allah yayiwa tsohon gwamnan Gombe, Hashidu rasuwa

Kakakin yan sandan jihar Imo, Mista Andrew Enwerem yace yan sanda na bincike akan kisan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel