Fadar Shugaban 'Kasa ta roƙi Majalisar Tarayya kan amincewa da buƙatar Buhari ta kasafin zaben 2019

Fadar Shugaban 'Kasa ta roƙi Majalisar Tarayya kan amincewa da buƙatar Buhari ta kasafin zaben 2019

Mun samu rahoton cewa fadar shugaban kasa ta nemi majalisar dokoki ta tarayya akan ta dakatar da hutun ta na jikiri domin samun dama ta amincewa da buƙatun shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da ya nema a gare ta.

Majalisar dai ta shirya shiga hutun dakatar tare da jinkirta zamanta a ranar Alhamis din da ta gabata, sai dai ta afka wannan hutu cikin gaggawa a ranar Talata sakamakon zanga-zangar rashin amincewa da takkadamar hana shige da fice na Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki da kuma mataimakin sa, Ike Ekweremadu a gidajen su

Rahotanni sun bayyana cewa ranar Talatar da gabata ne jami'an tsaro na 'yan sanda da DSS suka yiwa gidajen shugabanni biyun ƙawanya tare da hana shige da fice a bisa zargin da ake yi na hana ficewar sanatocin APC daga jam'iyyar.

Fadar Shugaban 'Kasa ta roƙi Majalisar Tarayya kan amincewa da buƙatar Buhari ta kasafin zaben 2019

Fadar Shugaban 'Kasa ta roƙi Majalisar Tarayya kan amincewa da buƙatar Buhari ta kasafin zaben 2019

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, fadar shugaban ƙasa na neman majalisar ta amince da buƙatar shugaba Buhari da sanadin hukumar zabe ta ƙasa dangane da kasafin da take neman tanadin su na gudanar da zaben 2019.

Shugaba Buhari a kwana-kwanan nan ya nemi majalisar akan tatso tare da fitar da N228bn cikin kasafin kudin manyan aikace-aikace da ta kayyade na N57bn a kasafin kudin 2018.

KARANTA KUMA:

Legit.ng ta fahimci cewa, hukumar zaben ta kasa watau INEC da hukumomin tsari na kasa na da buƙatar Naira Biliyan 242 domin gudanar da zaben 2019 da ya sanya shugaba Buhari ya nemi majalisar ta tanadar da wani kaso na wannan kudade cikin kasafin kudin 2018.

Fadar ta shugaban kasa a ranar Alhamis din da ta gabata ta miƙa ƙoƙon ta na bara akan ta zauna wajen amincewa da buƙatar ta shugaba Buhari domin amfanin kasa baki daya.

Hadimi na musamman ga shugaba Buhari akan harkokin majalisar tarayya, Sanata Ita Enang, shine ya bayyana haka yayin ganawa da manema labarai a babban birnin tarayya na Abuja, inda ya yi gargadin cewa duk wani jinkiri da majalisar ta gudanar kan wannan bukata zai janyo babbar barazana ga wasu sassa na gwamnatin kasar nan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel