Yanzu Yanzu: Majalisar dokokin jihar Benue ta dakatar da kakakinta da aka tsige

Yanzu Yanzu: Majalisar dokokin jihar Benue ta dakatar da kakakinta da aka tsige

Majalisar dokokin jihar Benue ta dakatar da kakakinta da aka tsige, Mista Terkimbi Ikyange na tsawon watanni shida.

An dakatar da shi ne a ranar Juma’a, 27 ga watan Yuli bayan wani batu da shugaban masu rinjaye, Mista Avine Agbom ya gabatar sannan ya samu goyon bayan yan majisa 18.

Yan majalisan sun zargi Ikyange da kawo hargitsi a majalisar ta hanyar zuba jami’an yan sanda domin hana mambobin samun damar shiga majalisar.

Sannan kuma a take suka kira kwamishinan yan sanda domin yayiwa jami’ansa umurnin barin harabar majalisar saboda babu wani barazana ga rayuka ko dukiyoyi.

Da misalign karfe 8:00am, motocin yan sanda yak are ainahin mashigin majalisar dokokin jihar, inda suka hana yan majalisa 22 da suka tsige Terkimbi Ikyange shiga majalisar.

Yanzu Yanzu: Majalisar dokokin jihar Benue ta dakatar da kakakinta da aka tsige

Yanzu Yanzu: Majalisar dokokin jihar Benue ta dakatar da kakakinta da aka tsige

Yan majalisar sun kuma yi yunkurin shiga majalisar ta kofar baya amma sai suka tarar da yan sanda sun kuma kare wajen.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Allah yayiwa tsohon gwamnan Gombe, Hashidu rasuwa

Hakan ya kai ga musayar kalamu tsakanin su da mataimakin kwaminan yan sanda, Tajudeen Bakare, wanda ya jagoranci aikin.

Bakare ya fadama yan majalisan cewa bayanai da aka gabatar masa ya nuna cewa za’a karya doka da oda.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel