Da duminsa: 'Yan sanda dauke manyan bindigogi sun garkame majalisar jihar Benue

Da duminsa: 'Yan sanda dauke manyan bindigogi sun garkame majalisar jihar Benue

Rahotanni da muka samu sun bayyana cewa jami'an 'yan sandan Najeriya dauke da manyan bindigogi sun rufe majalisar jihar Benue.

Kamar yadda This Day ta wallafa, jami'an 'yan sandan basu bayyana dalilin da yasa suka rufe majalisar ba. Sun kuma hana mambobin majalisar shiga harabara majalisar.

Da duminsa: 'Yan sanda dauke manyan bindigogi sun garkame majalisar jihar Benue

Da duminsa: 'Yan sanda dauke manyan bindigogi sun garkame majalisar jihar Benue

Wata majiya dake kusa da 'yan majalisar ta bayyana cewa rufe majalisar da akayi ba zai rasa nasaba da tsige Kakakin majalisar, Mr. Terkimbir Ikyange da akayi ba.

DUBA WANNAN: Kasashe 10 da suka fi talauci a nahiyar Afirka

An tsige Ikyange ne a farkon wannan makon.

Sai dai Ikyange yaki amincewa da tsigewar da a kayi masa, yaci majalisar bata bi ka'idodojin da ya kamata ba wajen tsige shi.

Ku biyo mu don samun karin bayani ...

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel