Saraki na shirya wani wasa ta hanyar kin sauya sheka - Sagay

Saraki na shirya wani wasa ta hanyar kin sauya sheka - Sagay

Farfesa Itse Sagay (SAN) shugaban kwamitin ba shugaban kasa shawara akan yaki da rashawa (PACAC) ya bayyana yan majalisar tarayya da suka sauya sheka daga jam’iyyar APC mai mulki zuwa jam’iyyar adawa ta PDP a matsayin zazzabin cizon sauro dake sanya APC ciwo tun shekaru uku da suka gabata.

Da yake bayyana ficewarsu a matsayin sauki ga APC, Sagay wadda yayi magana da jaridar Daily Independent yace yana mamakin cewa Bukola Saraki, shugaban majalisar dattawa ya zabi cigaba da kasance a jam’iyyar cewa bai gane wani irin wasa Saraki ke kokarin bugawa ba.

Saraki na shirya wani wasa ta hanyar kin sauya sheka - Sagay

Saraki na shirya wani wasa ta hanyar kin sauya sheka - Sagay

Ya kara da cewa kudirin yan majalisan shine su kunyata shugaban kasa Buhari a zaben 2019, cewa basu san bazasu iya maimaita abunda ya faru a 2014 ba lokacin da suka bar PDP zuwa APC.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Jihar Imo na cikin alhini yayinda yan bindiga suka kashe jigon APC

A halin da ake ciki, tun bayan ficewar yan majalisun dokokin Najeriya kimanin hamsin daga APC sun zuwa PDP ake ta tataburza tsakanin manyan jam’iyyun biyu game da shugancin majalisa, wanda a ka’ida majalisa mai rinyaje ce take shugabantar majalisun biyu.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Sanatoci guda 13 ne suka fice daga APC tare da yan majalisar tarayya guda 37, amma duk da haka, Sanatocin APC na ikirarin sune masu rinjaye a majalisar, don haka suka fara tayar da balli akan lallai sai sun sauya shugabancin majalisun biyu saboda basu yarda da shuwagabannin ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel