Gwamnatin Najeriya za ta kaddamar da sabon tsarin huldar jakadanci da kasashen waje

Gwamnatin Najeriya za ta kaddamar da sabon tsarin huldar jakadanci da kasashen waje

Mun samu labari daga Daily Trust cewa Mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II zai tsarawa wannan Gwamnati ta Shugaban kasa Muhammadu Buhari manufofin da za ta tafiyar da harkokin ta da sauran kasashen ketare na waje.

Gwamnatin Najeriya za ta kaddamar da sabon tsarin huldar jakadanci da kasashen waje

Sarki Sanusi II za su tsarawa Najeriya tsarin huldar jakadanci na kasa-da-kasa

Mataimakin Shugaban kasa Mai Girma Farfesa Yemi Osinbajo zai kaddamar da wani shiri da zai taimakawa tsarin huldar jakandacin Najeriya. Har da Mai Martaba Sarkin Kano watau Muhammadu Sanusi II aka tsara wannan shiri.

Wata Kungiya ta masana harkar huldar jakadanci a Najeriya mai suna AFRPN ta bayyana cewa Sarkin Kano kuma Tsohon Gwamnan babban Bankin Najeriya zai sa hannun sa wajen wannan tsari da Gwamnati za tayi aiki da shi.

KU KARANTA: Ka ji irin wasu bakin akidun 'Yan darikar Hakika

Shugaban Kungiyar ta AFRPN Ambasada Gani Lawal ya bayyana mana wannan jiya a Birnin Tarayya Abuja. Za dai a kaddamar da sabon tsarin da Gwamnatin Najeriya za tayi amfani da shi ta fuskar alaka da sauran kasashen waje.

Manyan Attajirai irin su Aliko Dangote, Alhaji Abdulsamad Isyaku Rabiu, Femi Otedola, da Mr Tunde Folawiyo za su kasance a wurin kaddamar da wannan tsari. Tsohon Minista Farfesa Bolaji Akinyemi zai kuma yi jawabi a wajen.

Ku na da labari cewa an hurowa Gwamnatin Tarayya wuta tayi maganin satar jama’a da fashi da makami da ake yi a Kasar nan. A halin yanzu kashe-kashen da ake yi musamman a Arewacin kasar yayi yawa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel