Kemi Adeosun: Shugaba Buhari ya gaza daukar mataki game da Ministar kudi bayan makonni

Kemi Adeosun: Shugaba Buhari ya gaza daukar mataki game da Ministar kudi bayan makonni

- Shugaban Kasa Buhari yace za a hukunta duk wasu marasa gaskiya

- Buhari komai girman mutum bai fi karfin doka tayi aiki a kan sa ba

- Sai dai har yanzu ba a dauki mataki kan zargin da ke kan Adeosun ba

Wasu sun fara kiran cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi amai ya lashe inda ya gaza daukar wani mataki game da zargin da ke kan wuyar daya daga cikin Ministocin sa watau Kemi Adeosun duk da yaki da rashin gaskiyar sa.

Kemi Adeosun: Shugaba Buhari ya gaza daukar mataki game da Ministar kudi bayan makonni

Shugaba Buhari yace zai hukunta masu laifi amma Ministar sa ta sha

A Ranar Laraba ne Shugaba Buhari ya bayyana cewa duk wanda aka samu da rashin gaskiya za a hukunta sa a Najeriya. Sai dai kusa mako 3 kenan yanzu ana zargin Ministar kudin kasar da amfani da takardun shaidar bautar kasa na bogi.

KU KARANTA: Shekarau yayi magana game da komawar sa APC

Duk da irin kiran da Jama’a su kayi na a binciki Kemi Adeosun, Shugaban kasar bai yi komai ba. Kungiyoyi da dama sun fara kiran a tsige Ministar a kuma yi kwakkwaran bincike game da lamarin na ta amma ba ayi komai ba har yau.

Buhari ya saba alkawarin da ya daukarwa ‘Yan Najeriya a baya inda ya sha alwashin binciken duk wani Ministan sa da aka samu da rashin gaskiya. A baya dai mun ji cewa Shugaban kasar ya sa a binciki Ministar amma har yau babu labari.

Shugaban Kasar ya bayyana wannan ne a dalilin binciken da ake yi kan Shugabannin Majalisun kasar. Kwanaki dai kun ji labari cewa wata Kungiyar Yarbawa tace ‘Yan bakin-ciki ne ke nema su taso Kemi Adeosun a gaba saboda irin kokarin ta.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel