Da sauran rina a Kaba: Sanatoci da yan majalisun APC sun hada kai don kawar da Saraki da Dogara

Da sauran rina a Kaba: Sanatoci da yan majalisun APC sun hada kai don kawar da Saraki da Dogara

Tun bayan ficewar yan majalisun dokokin Najeriya kimain hamsin daga APC sun zuwa PDP ake ta tataburza tsakanin manyan jam’iyyun biyu game da shugancin majalisa, wanda a ka’ida majalisa mai rinyaje ce take shugabantar majalisun biyu.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Sanatoci guda 13 ne suka fice daga APC tare da yan majalisar tayarra guda 37, amma duk da haka, Sanatocin APC na ikirarin sune masu rinjaye a majalisar, don haka suka fara tayar da balli akan lallai sai sun sauya shugabancin majalisun biyu saboda basu yarda da shuwagabannin ba.

KU KARANTA: Da dumi dumi: Buhari ya sabunta lasisin mallakar rijiyoyin mai guda 25

Da sauran rina a Kaba: Sanatoci da yan majalisun APC sun hada kai don kawar da Saraki da Dogara

Saraki da Dogara

Duk dayake shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki da Kaakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara yan APC ne, amma Sanatocin na APC na yi musu kallon basa tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari, kuma zasu iya komawa PDP, don haka suke bukatar tsigesu daga mukaman nasu.

Wata hujja da Sanatocin suke amfani da shi shine batun da ake yi na cewa wai Saraki nada hannu cikin harin da wasu yan fashi suka kai garin Offa na jihar Kwara dauke da muggan makamai, inda sama da mutum 30 suka mutu kamar yadda Yansanda ke zarginsa.

Haka zalika suna zargin Saraki da kin karanta wasikar da wasu Sanatoci guda uku suka mika masa na cewa zasu fita daga PDP zuwa APC, Sanatocin da suka hada da Hope Uzodinma, Fatima Raji Rasaki da Sunday Ogbuoji.

Guda cikin Sanatocin ya zanta da jaridar The Nation yana cewa: “Da sauran rina a kaba, muna da tabbacin mune masu rinjaye a majalisa, don idan ka cire Saraki muna da Sanatoci 53 a yanzu haka, mu magoya bayan Buhari muna tattaunawa don ganin mun cigaba da rike rinjaye a majalisun biyu, muna fatan zamu karu zuwa 57.

“A yanzu kawai muna jira ne mu ji Saraki da Dogara sun sanar da ficewarsu daga APC, a nan ne zamu tubure sai sun sauka, don haka sai mu yi amfani da rinjayen da muke da shi mu zabi sabbin shuwagabannin, babu gudu babu ja da baya game da wannan.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel