PDP na wata shiri na musamman don tarbar wadanda suka dawo jam'iyyar - Ologbondiyan

PDP na wata shiri na musamman don tarbar wadanda suka dawo jam'iyyar - Ologbondiyan

- Jam'iyyar adawa ta PDP tace zata karbi dukkan wadanda suka dawo jam'iyyar da hannu biyu-biyu

- A halin yanzu, jam'iyyar na shirya taron kwamitin gudanarwar jam'iyyar na musamman don maraba da sabbin mambobin

- Mai magana da yawun jam'iyyar PDP, Kola Ologbondiyan yace suna sa ran wasu gwamnonin zasu dawo jam'iyyar

Rahotanni da muka samu sunce jam'iyyar adawa ta PDP tana shirya taron kwamitin gudanarwar jam'iyyar na musamman don maraba da sabbin mambobin APC da suka sauya sheka zuwa PDP.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa ba'a tsayar da rannan wannan taron na musamman ba amma mai magana da yawun jam'iyyar PDP, Kola Ologbondiyan yace an sanar da masu jiga-jigan jam'iyyar game da taron.

PDP na wata shiri na musamman don tarbar wadanda suka dawo jam'iyyar - Ologbondiyan

PDP na wata shiri na musamman don tarbar wadanda suka dawo jam'iyyar - Ologbondiyan

A cewar Ologbondiyan, jam'iyyar tana maraba da dukkan sabbin mambobin ba tare da tsangwama ko nuna banbanci ba.

KU KARANTA: An gurfanar da wani lebura da ya fyade matar makwabcinsa

"Muna shirya taron kwamitin gudanarwa na musamman domin tarbar sabbin mambobin da suka dawo jam'iyyar mu. Muna son muyi musu maraba ta musamman saboda yanzu ne suka dawo gida.

"Kar ku manta cewa wadannan mutanen sun fito ne daga Majalisar dattawa da Majalisar wakilai saboda haka ya dace ayi musu tarba ta musamman. Hakan yasa muka shirya taron kwamitin gudanarwa ta musamman don yi musu maraba.

"A halin yanzu, akwai wasu gwamnoni da suke niyyar dawowa PDP. Muna tattaunawa dasu.

"Mu yanzu muna cike da murna saboda muna karbar sabbin zuwa cikin farin ciki yayin da masu adawa damu suna cikin kunci," inji Ologbondiyan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel