INEC ta mikawa PDP wasu bayanan sirri - zargin wasu lauyoyin daga bangaren APC

INEC ta mikawa PDP wasu bayanan sirri - zargin wasu lauyoyin daga bangaren APC

- A zaben da aka gama na Ekiti an kai ruwa rana tsakanin APC da PDP

- Lauyoyin Fayemi sun ce INEC ta mikawa PDP bayanan sirri

- AN kusa rantsar da Fayemi a matsayin gwamna

INEC ta mikawa PDP wasu bayanan sirri - zargin wasu lauyoyin daga bangaren APC

INEC ta mikawa PDP wasu bayanan sirri - zargin wasu lauyoyin daga bangaren APC

Lauyoyin Dan takarar gwamnan jihar Ekiti da ya lashe zaben, Kayode Fayemi, sun zargi hukumar INEC da ba lauyoyin PDP takardun zaben da aka yi a 14 ga watan yuli ba tare da sanar da sauran jam'iyyun ba.

Daya daga cikin lauyoyin Fayemi, Mista Tajudeen Akingbolu, yace jam'iyyar shi ta rubuta wasika ga INEC ta bukatar takardun CTC na zaben, inda suka hana.

Akingbolu yace takardun da suka bukata sun hada da EC8A,EC8B,EC8D,EC8E da sauran su, wanda ya jawo mamakin dalilin da yasa INEC ta ba PDP takardun ba tare da sanin sauran jam'iyyun ba.

Yace abinda aka saba yi shine ana sanar da sauran jam'iyyun siyasa duk lokacin da aka ba jam'iyya daya takardun zabe, kuma lauyoyin sauran jam'iyyun dole su kasance a gurin, domin gujewa canza abinda ke rubuce ko lalata takardun.

DUBA WANNAN: Komawar Shekarau da Takai APC, bayanai

Akingbolu da yayi magana da majiyar mu a Ado-Ekiti a ranar Alhamis yace yaje ofishin INEC don gani REC, Farfesa Abdulganiyu Raji, domin jin cigaban da aka samu amma an sanar dashi baya kana kujerar shi.

A lokacin da muka tuntubi mai magana da yawun INEC, Mista Taiwo Gbadegesin, yaki tofa albarkacin bakin shi. "REC Abdulganiyu ne zai yi magana akan cigaban da aka samu" inji Mista Taiwo.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel