Dalilan da suka hana ni halartar taron ganawa na Sanatocin APC da shugaba Buhari ba - Adeyeye

Dalilan da suka hana ni halartar taron ganawa na Sanatocin APC da shugaba Buhari ba - Adeyeye

Daya daga cikin sanatocin jam'iyyar APC da ba su samu damar halartar taron ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari, Sanata Olusola mai wakilcin jihar Osun ta Tsakiya, ya bayyana dalilin rashin sa a wannan taro.

Kamar yadda shafin jaridar Premium Times ya ruwaito, Mr Adeyeye ya bayyana cewa, ya samu sakon ganawar ne a kurarren lokaci da ya sanya ya gaza samun sukunin halartar taron.

Rahotanni sun bayyana cewa, Sanatoci 39 na jam'iyyar APC a ranar Larabar da ta gabata sun gana tare da shugaban kasa a fadar sa ta Villa domin tabbatar da goyon bayan su a gare shi.

Legit.ng ta fahimci cewa, wannan ganawa ta biyo bayan sauya sheka tare da ficewar wasu sanatoci 14 daga jam'iyyar APC a ranar Talatar da ta gabata, inda 13 cikin wannan sanatoci sun koma karkashin inuwar jam'iyyar adawa ta PDP.

Dalilin da ya sa ban halarci taron ganawa na Sanatocin APC da shugaba Buhari ba - Adeyeye

Dalilin da ya sa ban halarci taron ganawa na Sanatocin APC da shugaba Buhari ba - Adeyeye

Cikin wata sanawar a shafin sa na dandalin sada zumunta, Mista Adeyeye ya bayyana cewa, sakon wannan ganawa ya isar masa ne a yayin da yake gabatar da wata lacca a babbar Kwalejin lafiya ta jami'ar Ibadan.

KARANTA KUMA: 2019: Zan goyi bayan duk wani dan takara da zai kai Najeriya ga gaci - Obasanjo

Sanatan ya ci gaba da cewa, an shirya wannan taro na jami'ar tun tsawon watanni biyar da suka gabata kuma bugu da kari ba bu dama ta tunkarar birnin tarayya a daidai wannan kurarren lokaci.

Sanatan ya kuma bayar da shaidar cewa, Sanatocin na jam'iyyar APC su na da cikakkiyar masaniya ta uzurin sa a birnin na Ibadan, ba ya ga haka kuma ya aika da sakon neman afuwar shugaban kasa dangane da rashin halartar taron.

Domin kaucewa shakku, Sanatan ya bayar da tabbacin sa da cewa, har ila yau yana sanye da rigar sa ta jam'iiayr APC.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel