Babu wanda zamu bawa tikiti hannu-daya babu zaben cikin gida - Oshiomhole

Babu wanda zamu bawa tikiti hannu-daya babu zaben cikin gida - Oshiomhole

Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Kwamared Adams Oshiomhole yace jam'iyya ba zata lamincewa bayar da tikitin zabe ba tare da hamayya ba ga 'yan majalisar APC don kawai ana kwadayin su cigaba da zama a jam'iyyar.

Oshiomhole ya yi wannan furucin ne a jiya Alhamis a taron da ya yi da jiga-jigan jam'iyyar APC na Majalisar Wakilai na kasa a sakatariyar jam'iyyar dake Abuja.

Yace abinda jam'iyyar kawai zata iya yi shine bawa kowa damar fitowa takara don fafatawa a zaben fidda gwani don a gane wanda jama'a su kafi kauna.

Babu wanda zamu baiwa tikiti hannu-daya babu zaben cikin gida - Oshiomhole

Babu wanda zamu baiwa tikiti hannu-daya babu zaben cikin gida - Oshiomhole

A karshen taron, yace jam'iyyar za tayi amfani da irin salon zaben fidda gwani kai tsaye da akayi amfani dashi a jihohin Osun da Bauchi wajen zaben 'yan takara.

DUBA WANNAN: An gurfanar da wani lebura da ya fyade matar makwabcinsa

Oshiomhole yace, Dole jam'iyyar APC ta dage wajen fidda Sanatoci masu nagarta duk da cewa jam'iyyar za tayi la'akari da kwarewar aiki.

A jawabin da ya yi bayan taron, shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila yace sun kai ziyarar ne saboda su tabbatar wa jam'iyyar goyon bayansu.

Yace ficewar wasu 'yan majalisa daga jam'iyyar ba zai sa su karaya ba domin a yana kyautata zaton wasu daga cikin wadanda suka fice zasu dawo jam'iyyar daga baya.

Gbajabiamila yace jam'iyyar zata cigaba da bawa 'yan majalisa dukkan goyon bayan da suke bukata musamman sabon shiga a majalisar don taimaka musu da shawarwari kan yadda zasu kawo cigaba ga yankunan da suke wakilta.

Sai dai Kakakin majalisar, Dogara Yakubu da mataimakinsa Yusuf Lawan basu hallarci taron ba.

Sai dai Gbajabiamila ya yi musu uzuri inda yace babu mamaki wasu ayyukan ne suka hana su hallartar taron kuma ya kara da cewa cikin gaggawa aka sanar da batun kawo ziyarar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel