Masu sauya sheka na adawa ne da gwamnoni ba wai Buhari ba – Fadar shugaban kasa

Masu sauya sheka na adawa ne da gwamnoni ba wai Buhari ba – Fadar shugaban kasa

Fadar shugaban kasa a ranar Alhamis tace wadanda suka sauya sheka daga jam’iyyar All Progressives Congress ba wa da shugaban kasa Muhammadu Buhari suke adawa ba, sai dai da wasu gwamnoi da shugabannin APC a jihohinsu.

Babban madimin shugaban kasa kan harkoki majalisa, Sanata Ita Enang ya bayyana hakan a wata hira da manema labarai a Abuja.

Ya ce hiransa da mambobi majalisar dokoki a nuna cewa suna goyon bayan B uhari dari bisa dari da sake takararsa a 2019.

Masu sauya sheka na adawa ne da gwamnoni ba wai Buhari ba – Fadar shugaban kasa

Masu sauya sheka na adawa ne da gwamnoni ba wai Buhari ba – Fadar shugaban kasa

A ganawar daren ranar Laraba da aka yi tsakanin Buhari da sanatocin APC, jami’in fadar shugaban kasar ya bayana cewa wasu yan majalisa da suka sauya sheka sun sanar da sauya shekarsu ne zuwa wasu jam’iyyu ko kuma suka yi niyar sauya sheka sun dawo APC.

KU KARANTA KUMA: Yan Majalisar da suka koma PDP za su yiwa Buhari aiki ne — Fadar shugaban kasa

A taron, an tattaro cewa Buhari ya bukai masu ruwa da tsaki na APC a majalisar dattawa da su cigaba da rike matsayarsu na masu rijaye.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel