Ana tuhumar wani Sanatan jam’iyyar PDP da amfani da takardun karatu na bogi

Ana tuhumar wani Sanatan jam’iyyar PDP da amfani da takardun karatu na bogi

Wata babbar kotun jihar Osun ta bada wa’adin kwanaki shidda ga dan takarar gwamnan jihar a karkashin inuwar jam’iyyar PDP, Sanata Adeleke Ademola don ya kawo mata shaidar kammala karatunsa na firamari, inji rahoton The Cables.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito ana tuhumar Adeleke wanda shine wakilin al’ummar Osun ta tsakiya a majalisar dattawa akan yin amfani da takardar karatun bogi, wasu yayan jam’iyyar, Rasheed Olabayo da Oluwaseun Idowu ne suka maka shi gaban kotu kan wannan zargi.

KU KARANTA: Hatsari ba sai a Mota ba: Mutane 5 sun gamu da ajalinsu yayin da Kwalekwale ta kifa dasu

A satin data gabata ne Adeleke ya kada abokin hamayyarsa, Akin Ogunbiyi, sai dai Rasheed d Idowu sun ce Adelek ya bayyana ma hukumar zabe takardar shaidar kammala karatun Firamari na bogi, wanda hakan karan tsaye ne ga sashi na 177 na kundin dokokin Najeriya.

Ana tuhumar wani Sanatan jam’iyyar PDP da amfani da takardun karatu na bogi
Adeleke

Da wannan ne masu karar suka shaida ma Kotu bukatarsu, na cewa Kotu ta haramta ma jam’iyyar PDP mika sunan Adeleke ga hukumar INEC a matsayin dan takarar gwamnan da zai wakilci jam’iyyar a zaben gwamnan jihar da za ayi a watan Satumba.

Bayan sauraron bukatar masu shigar da kara, sai Alkalin Kotun, ya baiwa Sanata Adeleke alfarmar kwanaki shida ya bayyana ma Kotu sahihan shaidan dake nuna ya yi makarantar Firamari, sa’annan ya ja hankalin dukkanin bangarorin biyu da su mayar da wukarsu cikin kube har sa Kotu ta yanke hukunci.

“Sakamakon wannan lamari ne da ya shafi zaben, ina da tabbcin Jama’a zasu zura idanu don ganin yadda za ta kaya, don haka da zarar an shigar da magana gaban Kotu, ba a yarda wani ya sake daukar wani mataki ba ba tare da umarnin Kotu ba.” Inji shi.

Daga karshe Alkali Oladimeji y adage sauraron karar zuwa ranar 1 ga watan Agusta mai zuwa, sa’annan ya gargadi wani ake kara kan cewa Kotu ba za ta karbi wani uzurinsa ba matukar bai bayyana mata shaidun kammala karatunsa nasa ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel