2019: Zan goyi bayan duk wani dan takara da zai kai Najeriya ga gaci - Obasanjo

2019: Zan goyi bayan duk wani dan takara da zai kai Najeriya ga gaci - Obasanjo

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a ranar Alhamis din da ta gabata ya bayyana cewa, wadanda ke lalata kasar nan ba bu lallai su kasance mamugunta sai dai zababbun shugabanni masu rike da madafun iko da suka zuba idanu tare da yin shiru kan al'amurran da suka shafi kasar.

Obasanjo ya bayyana ire-iren wadannan mutane a matsayin makiya kasar nan ta Najeriya, inda ya sha alwashin ba zai rike bakin sa yayi shiru yayin da munanan al'amurra ke faruwa, sai dai ya ce a shirye yake ya goyi bayan duk wanda zai kai kasar nan ga gaci.

Dattijon na kasa ya yi wannan takaddama tare da kaddamar da matsayar sa yayin da tsohon ministan ayyuka na musamman, Kabiru Tanimu Turaki, ya ziyarci shi a gidan sa dake babban birnin Abeokuta a jihar Ogun.

2019: Zan goyi bayan duk wani dan takara da zai kai Najeriya ga gaci - Obasanjo

2019: Zan goyi bayan duk wani dan takara da zai kai Najeriya ga gaci - Obasanjo

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya bayyana, Turaki ya kai ziyara ne birnin Abeokuta domin bude sabon shafi tare da neman amincin da tabarraki na Obasanjo dangane da kudirin sa na neman takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2019.

KARANTA KUMA: Wani Hatsarin Mota ya salwantar da rayuka 2 a jihar Ogun

Obasanjo ya fahimci cewa, kasar Najeriya na da albarkar amintattun mutane nagari da ka iya jagoranci ko ina a fadin duniya, inda ya bayyana cewa ba zai gaza ba wajen fafutikar sa ta neman tsayayyen jagora da zai kai ta ga gaci.

A yayin haka kuma jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, Kungiyar Transparency International ta bayyana yadda shugabannin tsaro da gwamnonin jihohi ke karkatar da akalar dukiyar gwamnati ta kimanin N241bn a duk shekara.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel