Da dumin sa: Hukumar EFCC ta gurfanar da surukin Obasanjo kuliya

Da dumin sa: Hukumar EFCC ta gurfanar da surukin Obasanjo kuliya

Jami'an hukumar nan dake yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC a Najeriya ranar Alhamis sun gurfanar da wani mutum mai suna John Abebe dake zaman suruki ga tsohon shugaban kasar Najeriya Olusegun Obasanjo a kotu.

Mista John Abebe wanda kani ne ga marigayiya tsohuwar matar Cif Obasanjo, Stella Obasanjo din EFCC ta ce ta gurfanar da shi ne a kotun bisa zargin sa da suke yi da anfani da takardun bogi wajen neman aikin hakar mai daga Najeriya din.

Da dumin sa: Hukumar EFCC ta gurfanar da surukin Obasanjo kuliya

Da dumin sa: Hukumar EFCC ta gurfanar da surukin Obasanjo kuliya

KU KARANTA: Bayan ficewa daga APC gwamnan Benue ya rasa kusa a gwamnatin sa

Legit.ng ta samu cewa hukumar EFCC din ta bayyana hakan da yayi amatsayin babban laifi inda kuma ta bukaci kotun da ta hukunta shi.

A wani labarin kuma, Rahotannin da muke samu daga babban bankin Najeriya yana nuni ne da cewa baitul-malin kasar Najeriya na ta cigaba da raurayewa a watanni uku da suka shude a jere kamar dai yadda alkalumman da suka fitar jiya suka nuna.

Rahoton da babban bankin ya fitar dai a ranar Larabar da ta gabata ya nuna cewa baitul-malin yanzu haka dalar Amurka biliyan 47.303 wanda yake nuna cewa dalar Amurka miliyan 394 ce ta zurare a kwanaki 13 kacal da suka gabata.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel