Da dumin sa: Mai taimakawa Gwamnan Benue yayi murabus daga mukamin sa

Da dumin sa: Mai taimakawa Gwamnan Benue yayi murabus daga mukamin sa

Labarin da muke samu yanzu da dumin sa daga majiyoyin mu sun tabbatar mana da cewa mai taimakwa Gwamnan jihar Benue dake a Arewacin Najeriya akan harkokin yada labarai mai suna James A. Ornguga ya yi murabus daga mukamin sa.

Wannan dai na kunshe ne a cikin takardar da ya aikewa Sakataren gwamnatin jihar dauke da sa hannun sa a ranar Alhamis, 26 ga watan July na shekarar 2018 yana kuma mai godewa gwamnan da sauran al'ummar jihar bisa damar da ya samu na yin aiki.

Da dumin sa: Mai taimakawa Gwamnan Benue yayi murabus daga mukamin sa
Da dumin sa: Mai taimakawa Gwamnan Benue yayi murabus daga mukamin sa

KU KARANTA: Dangote yayi kyautar Naira miliyan 300

Legit.ng ta samu cewa Mista James A. Ornguga ya bayyana cewa yayi murabus din ne domin ya samu damar cigaba da siyasar sa.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa Gwamnan jihar ta Benue din Mista Samuel Ortom ya fice daga jam'iyyar APC ya zuwa jam'iyyar PDP jiya.

A wani labarin kuma, Shugaban masana sararin samaniya da kuma hasashen yanayi a jami'ar tarayyar Najeriya dake a garin Nsukka, Farfesa Augustine Ubachuku yayi hasashen cewa a gobe Juma'a wata zai yi masassarar da bai taba yi ba mai tsawon gaske.

Farfesa Ubachuku ya bayyana hakan ne a lokacin da yake fira da manema labarai a dakin taron jami'ar da safiyar yau, inda kuma ya shawarci al'umma da su kwantar da hankalin su.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng