Zargin N3.2b: Kalu zai san makomar sa a ranar 31 ga watan Yuli

Zargin N3.2b: Kalu zai san makomar sa a ranar 31 ga watan Yuli

Alakalin babbar kotun tarayya da ke Legas, Mohammed Idris ya sanya ranar 31 ga watan Yuli cewa zai yanke hukuncin makomar tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Uzor Kalu.

Ana zargin Kalu da yin harkallar naira biliyan 3.2. Sauran wadanda ake tuhuma tare da shi sun hada da kwamishinan kudi na lokacin sa, Jones Udeogu da kuma kamfanin Slok Nigeria Ltd., mallakar Kalu.

Kalu ya nusar da alkalin cewa akwai wata aya mai lamba 126 da ke cikin Dokar Gabatar da Shaidu.

Dokar ta ce ana amfani da shaida ce wadda mai bada shaida ya bayyana da kan sa ido-na-ganin-ido ya gabatar a kotu.

Zargin N3.2b: Kalu zai san makomar sa a ranar 31 ga watan Yuli

Zargin N3.2b: Kalu zai san makomar sa a ranar 31 ga watan Yuli

Ya ce shaida mai lamba D14 da kuma D1 wadda EFCC ta bayar, ta na dauke ne da sa hannun jami’in EFCC maimakon sa hannun wani jami’in banki, tunda daga banki EFCC ta ce ta samo shaidar.

A kan haka ne ya nemi Mai Shari’a ya kori karar.

KU KARANTA KUMA: Ina iya barin jam’iyyar APC – Gwamnan jihar Kwara

Lauyan EFCC, Rotimi Jacobs ya sanar da kotu cewa akwai aiki ja a gaba, saboda ba duka shaidun ba kenan.

Sakamakon haka sai alkalin ya ce a ba kotu ako guda saboda ta yi tunani akan shaidun. Zuwa ranar 31 ga watan Yuli, za ta yanke hukunci a kan wannan kiki-kakar.

Idan ka na da shawara ko wata bukata, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku neme mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel