Oshiomole na dinke barakar APC, mun amince da shugabancinsa – Shehu Sani

Oshiomole na dinke barakar APC, mun amince da shugabancinsa – Shehu Sani

Sanata Shehu Sani mai wakiltan Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa ya jaddada cewa yana nan cikin jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Game da cewar sashen yada labarain jam’iyyar, Shehu Sani ya bayyana hakan ne yayin tattaunawa da yan jarida a sakatariya jam’iyyar APC a yau Alhamis bayan ganawa da shugaban jam’iyyar, Adams Oshiomole.

Yace: “Mun yi imani cewa sabon shugabancin jam’iyyar na ida ikon kawo karshen rashin adalci,”

“A cewar Frantz Fanan. ‘Munyi tawaye ne saboda mun kasa nishi’. Saboda haka mun yi tawaye ne saboda yadda ake gudanar da jam’iyyar na hana nufasawa. Yanzu muna da likita mai tiyata wand ake iyakan kokarinsa wajen dinke Baraka. Shi yasa muke bashi dama yin hakan.”

Da aka tambayeshi kan kasancewa dan jam’iyyar, Sani yace: “Tun ku ga gan ni a nan, ni dan jam’iyya ne. Idan nib a dan jam’iyyar ba ne, ba zaku gan ni a sakatariyan jam’iyyar ba.”

KU KARANTA: Tambuwal zai koma PDP makon gobe – Majiya mai karfi

Shehu Sani ya kasance daya daga cikin masu sukan shugabancin shugaba Muhammadu Buhari. Kuma saboda rikicin da ke tsakaninsa da gwamna Nasir El-Rufa’I, an dade ana kyautata zaton zai koma jam’iyyar PDP.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel