Tambuwal zai koma PDP makon gobe – Majiya mai karfi

Tambuwal zai koma PDP makon gobe – Majiya mai karfi

Bayan makonnin tattuanawa da shugabannin jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP, gwamnan jihar Sokoto zai sauya sheka jam’iyyar adawan a makon gobe.

Kamar yadda abubuwa ke gudana a yanzu, majiya mai karfi da ke kusa da tsohon kakakin majalisar wakilan, wanda aka zaba gwamnan jihar Sokoto a karkashin jam’iyyar APC zai sauya sheka jam’iyyar PDP.

A makon jiya, Tambuwal da gwamnan jihar Kwara, Abdulfatah Ahmed, ya gana da shugabannin jam’iyyar PDP.

Yayinda ake has ashen cewa yana neman kujeran takaran shugaban kasa a 2019 ne, da alamun Tambuwal na da rashin jituwa da fadar shugaban kasa bisa ga wasu jawabai da yayi kwanakin nan na sukan gwamnatin shugaba Buhari.

Tambuwal zai koma PDP makon gobe – Majiya mai karfi

Tambuwal zai koma PDP makon gobe – Majiya mai karfi

A kwanakin baya, wasu yan bindiga sun kaiwa cibiyar daular Islamiyyan mumunan hari inda akalla mutane 35 suka rasa rayukansu, dukiyoyi da kuma muhallansu.

A jawabin da gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya saki, ya daura laifin wannan hari kan gazawar shugaba Muhammadu Buhari inda yace “gazawan shugabanci” ne duk da tawan makudan kudaden da ake kashewa wajen samar da tsaro.

KU KARANTA: Wasu Sanatocin zasu sake komawa APC bayan ficewarsu

Majiyar tace: "Wannan hari da aka kaiwa Sokoto wani mataki ne na wasu domin kawar da hankalin gwamnan daga takara kujeran shugaban kasa a 2019. Amma gwamnan ya riga ya daura niyyarsa. Zai fita daga APC ya koma PDP ranan Lahadi."

Read more at: https://www.vanguardngr.com/2018/07/tambuwal-to-defect-to-pdp-next-week/

A jiya Laraba, 25 ga watan Yuli, gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP duk da tattaunawan sulhu da sukayi da shugabannin jam'iyyar APC a Abuja.

A yau kuma, gwamnan jihar Kwara, AbdulFatah Ahmed ya bayyana niyyan sauya sheka a kaikaice.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel