Rundunar sojin saman Najeriya ta cafke gawurtattun 'yan bindiga 16 a Zamfara

Rundunar sojin saman Najeriya ta cafke gawurtattun 'yan bindiga 16 a Zamfara

Dakarun jami'an sojin saman Najeriya na rundunar ko-ta-kwana ta 207 watau Quick Response Group (QRG) a garin Gusau sun sanar da samun nasarar cafke wasu gawurtattun 'yan bindiga guda sha shida a wani samamen da suka kai masu a dokar daji.

Babban kwamandan rundunar Kaftin Caleb Olayera shine ya sanar da hakan lokacin da yake karbar bakuncin babban hafsan rundunar sojin saman kasar Air Marshal Sadique Abubakar da ya kai masu ziyarar aiki.

Rundunar sojin saman Najeriya ta cafke gawurtattun 'yan bindiga 16 a Zamfara

Rundunar sojin saman Najeriya ta cafke gawurtattun 'yan bindiga 16 a Zamfara

KU KARANTA: Jarumai mata 5 da suka fi tsada a masana'antar Kannywood

Legit.ng ta samu cewa babban hafsan rundunar sojin saman kasar Air Marshal Sadique Abubakarya yaba wa dakarun musamman ta yadda suka sadaukar da rayuwar su wajen tabbatar da tsaro.

A wani labarin kuma, Shahararren mai kudin nan na nahiyar Afrika kuma dan asalin jihar Kano, Alhaji Aliko Dangote ya gina tare kuma da damka wani katafaren gini da ya lakume zunzurutun kudi har Naira miliyan 300 ga jami'ar tarayya ta Ibadan domin koyo da koyarwar dabarun kasuwancin zamani.

Haka ma dai fitaccen mai kudin wanda babban daraktan zartaswar rukunin kamfanonin na Dangote, Mansur Ahmed ya wakilta, ya kuma sha alwashin cigaba da kaddamar da ire-iren wadannan ayyukan alherin a kasar baki daya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel