An sace wani limamin coci a jihar Kogi

An sace wani limamin coci a jihar Kogi

Wasu 'yan bindiga da har yanzu ba a tabbatar da su waye ba sun sace babban limamin cocin Catholica na St. Michael, a Obajana dake jihar Kogi, mai suna Rev. Fr. Leo Michael

An sace wani limamin coci a jihar Kogi

An sace wani limamin coci a jihar Kogi
Source: Depositphotos

Wasu 'yan bindiga da har yanzu ba a tabbatar da su waye ba sun sace babban limamin cocin Catholica na St. Michael, a Obajana dake jihar Kogi, mai suna Rev. Fr. Leo Michael.

Wani babban Fasto na cocin Catholic Diocese, Rev. Fr. Peter Adinoyi, shine ya bayyanawa manema labarai afkuwar lamarin a garin Lokoja yau dinnan.

DUBA WANNAN: Tayi wurgi da gawar mijinta waje, tace ba za'a ajiye mata gawa a daki ba

Ya ce Faston yana dawowa daga Okene zuwa Obajana a lokacin da aka sace shi din, a dai dai Kauyen Irepeni dake kan hanyar Okene zuwa Lokoja. A cewar shi an gabatar da rahoton sace limamin ga ofishin 'yan sanda na kauyen Irepeni.

Bayan haka, Adinoyi ya ce a ranar 25 ga watan nan 'yan bindigar sun kira mambobin cocin limamin, inda suka bukaci a basu naira miliyan 50, kafin su saki Faston. Ya ce daga baya sun rage kudin zuwa miliyan 20, har ya dawo miliyan 8.

Adinoyi ya ce 'yan bindigar sun bawa mambobin cocin zuwa karfe daya na ranar yau akan su gabatar da kudin ko kuma suki sakin Faston.

Ya ce mutanen cocin sun kasa hada kudin, inda suka kira hukumar tsaro akan su taimaka wurin ceto rayuwar limamin.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel