Kashi 40% na mutanen Najeriya na fama da matsalar ruwa mai tsabta

Kashi 40% na mutanen Najeriya na fama da matsalar ruwa mai tsabta

- Ana matukar fama da matsalar ruwa mai tsabta yanzu a Najeriya

- Haka kuma al’ummar na kuka da karancin muhalli mai tsabta

Kashi 40% na mutanen Najeriya na fama da matsalar ruwa mai tsabta

Mutanen Najeriya na kuka da rashin ruwa mai tsabta

Mun samu labari cewa Gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta bayyana cewa kusan kashi 70% na jama’ar kasar su na fama da tsabtataccen muhalli da ruwa mai tsabta. Ma’aikatar ruwa na Kasar ta bayyana wannan.

Dr. Ibrahim Musa wanda babban Jami’in Ma’aikatar ruwa na kasar ya nuna cewa ana fama da matsalar muhalli mai tsabta da kuma ruwa mai kyau. Sama da kashi 40% na mutanen Najeriya na fama da kalubalen lafiyayyen ruwan sha.

KU KARANTA:

A wajen wani taron bita da aka yi yau a Birnin Tarayya Abuja ne wannan Sakataren na din-din-din ya koka da wannan matsala. Kungiyar SDG ta Majalisar dinkin Duniya na kokarin hada-kai da Gwamnatin kasar na shawo kan wannan matsala.

Gwamnatin Tarayyar tayi wannan jawabi ne ta bakin Ibrahim Musa wanda shi ne babban Sakataren Ma’aikatar harkokin ruwa. A dalilin wannan matsala ne aka shirya bita domin ganin an inganta tsabtar ruwan sha da na wurin zama a cikin fadin kasar.

Kun ji labari jiya cewa ana shirin gina wani matatar man fetur a Jihar Katsina. Talban Katsina watau Zakari Ibrahim ne zai bude wannan kamfanin na tatar man fetur a Arewacin Kasar a Garin Mashi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel