Wata kotun kasar Amurka ta yanke hukunci kan karar da ‘yan Biyafra suka shigar da gwamnatin Najeriya

Wata kotun kasar Amurka ta yanke hukunci kan karar da ‘yan Biyafra suka shigar da gwamnatin Najeriya

Wata kotun kasar Amurka dake zamanta a birnin Washington DC tayi watsi da karar da masu fafutikar kafa kasar Biyafra suka shigar da gwamnatin Najeriya gabanta.

Kungiyar ta Biyafra, ta hannun lauyanta, Godson M. Nnaka, na neman gwamnatin Najeriya ta biya ta kaso 40%, kimanin dalar Amurka miliyan $550m, daga kudin Abacha da aka karbo daga kasar Switherland.

Daga cikin wadanda kungiyar Biyafra din ta shigar kara tare da gwamnatin Najeriya sune; shugaban sojojin kasa, Janar Tukur Buratai, shugaban hukumar tsaro ta DSS, Lawan Daura, tsohon shugaban rundunar ‘yan sanda, Solomon Arase da kuma na yanzu, Ibrahim Idris.

Wata kotun kasar Amurka ta yanke hukunci kan karar da ‘yan Biyafra suka shigar da gwamnatin Najeriya

Wata kotun kasar Amurka ta yanke hukunci kan karar da ‘yan Biyafra suka shigar da gwamnatin Najeriya

Kungiyar ta shigar da karar ne bisa zargin take hakkin, azabtar wa tare da kasha mambobinta yayin da suke gudanar da zanga-zangar lumana a sassa daban-dabantsakanin shekarar 2016 da shekarar 2017.

Alkalin kotun, Dabney Friedrich, ya yi watsi da dukkan tuhumar da kuniyar ke yiwa gwamnatin Najeriya tare da shaida masu cewar mahunkuntan Najeriya na da kariya irinta diflomasiyya a kasashen ketare.

DUBA WANNAN: Fashin Offa: Tawagar 'yan sanda masu bincike sun bi Saraki har Ofis

Kungiyar Biayafra dai ta tayar da kayar baya a tsakanin 2016 da 2017 a yunkurinsu na ganin sun tage daga Najeriya tare da kafa kasar su ta 'yan kabilar Igbo.

Al'amuran kungiyar sun yi karfi lokacin da shugaba Buhari ke zaman jinya a wani asibitin kasar Ingila. Saidai bayan dawowarsa ya umarci sojoji su da ragowar jami'an tsaro su kwantar da tarzomar da tsagerun 'yan Biyafra ke tayarwa a yankin kudu maso gabashin Najeriya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel