An gurfanar da wani lebura da ya fyade matar makwabcinsa

An gurfanar da wani lebura da ya fyade matar makwabcinsa

A yau Alhamis ne aka gurfanar da wani lebura mai shara a banki, Essien Akpan, a gaban kotun majisatre dake Ajegunle a Legas bisa zarginsa da yiwa matar makwabcinsa fyade.

Ana tuhumar Akpan mazaunin gida mai lamba 19 Prince Fadin Street, Olodi-Apapa Legas bisa aikata laifi guda daya na fyade a gaban alkaliyar kotun, Mrs L.Y. Balogun.

Dan sanda mai shigar da kara, Saja Kokoye Olusegun yace lamarin ya afku ne a ranar 30 ga watan Mayun wannan shekarar misalin karfe 2 na dare a gidan wanda ke karar.

Yace Akpan ya tilastawa matar, mai yara hudu saduwa dashi.

An gurfanar da wani lebura da ya fyade matar makwabcinsa

An gurfanar da wani lebura da ya fyade matar makwabcinsa

Ya yi ikirarin cewa wanda ake tuhumar ya dade yana neman matar da soyaya amma bata amince ba.

KU KARANTA: Zurarewar $21: Majalisa ta gayyaci Baru, Kachikwu da shugabanin wasu hukumomi 2

A ranar da abin ya faru, matar da fito tsakar gida ne misalin karfe 2 na dare don ta kwashe kayaykin yaranta daga igiyar shanya saboda hadari ya taso ashe wanda ake tuhumar yana labe a bayanta.

Daga nan ne ya far mata kuma ya tilasta mata saduwa dashi. Tayi ta ihu na neman taimako amma babu wanda ya zo ya taimaka mata.

An kama wanda ake tuhumar ne bayan matar da sanar da mijinta abinda ya faru saboda a lokacin da abin ya faru ya yi tafiya.

A cewar mai shigar da karar, laifin ya sabawa sashi na 168(d) na dokar masu laifi na jihar Legas shekarar 2015.

Akpan ya musanta laifin da ake tuhumarsa da aikatawa kuma Mrs Balogon ta bayar da belinsa a kan kudi N50,000 tare da gabatar da mutane biyu da zasu tsaya masa.

An dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 7 ga watan Satumba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel