Kasawar Buhari fa kasawar Arewa ce baki daya - Dattijan Arewa

Kasawar Buhari fa kasawar Arewa ce baki daya - Dattijan Arewa

Sakataren kungiyar dattawan Arewa ta (ACF) Mr. Anthony Sani ya yi kira ga shugabanin siyasa na yankin arewa da su rika tsaftace alakarsu da shugaban Muhammadu Buhari saboda kada su kawo masa cikas wajen cinma nasaorin da yasa a gaba.

Kungiyar ta ACF ta bayyana rashin jin dadin ta game da irin abubuwan dake faruwa a fagen siyasa a kasar nan, inda tace laifin Arewa ne muddin Shugaba Muhammadu Buhari baiyi nasara ba.

Sani ya yi wannan tsokacin ne yayin da yake ganawa da tawagar Media Trust Limited da suka kawo masa ziyarar ta'aziyya game da rasuwar Ciyaman din kungiyar kuma tsohon Sufeta Janar na 'yan sanda, Alhaji Ibrahim Coomassie.

Laifin Arewa ne muddin shugaba Buhari ya gaza - ACF

Laifin Arewa ne muddin shugaba Buhari ya gaza - ACF

KU KARANTA: Canjin sheka: Sanatoci dake goyon bayan Saraki sunyi caa a kan Sanata Abdullahi Adamu

Yace kasancewar shugaban Muhammadu Buhari dan arewa kuma galibin masu rike da mukamman siyasa 'yan arewa ne ya dace shugabanin siyasar na Arewa su goya wa Buhari baya domin ya yi nasara.

"Saraki da Dogara duk 'yan arewa ne kuma jam'iyyarsu daya da shugaba Muhammadu Buhari. Ya kamata su taimakamasa ya yi nasara domin idan har ya gaza toh Arewa ce baki daya ta gaza," inji shi.

Da yake tsokaci a kan tsohon ciyaman din kungiyar, Sani yace rashin lafiyar Coomassie ya saka abubuwa sun tsaya cak a kungiyar domin kafin rashin lafiyansa, ya kasance shugaba ne mai azama da kokari.

Yace shugabanin kungiyar suna sa ran zai sami sauki kwatsam sai suka samu labarin rasuwarsa.

A bangarensa, Manajan yankin arewa na Media Trust Ltd, Danjuma Isa Oboni yace shi da tawagarsa sun ziyarci ACF ne don yiwa kungiyar ta'aziya bisa rasuwar tsohon shugabansu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel