Rikicina da El-rufai: Abun da shugaba Buhari ya fada mun - Shehu Sani

Rikicina da El-rufai: Abun da shugaba Buhari ya fada mun - Shehu Sani

Fitaccen Sanatan nan dake wakiltar mazabar jihar Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani ya bayar da karin haske game da rikicin sa da gwamnan jihar kuma jagoranta, Malam Nasir El-rufai inda yace da alamu yazo karshe.

Shehu Sani dai jim kadan bayan kammala taron su da shugaba Muhammadu Buhari a jiya ya ce shugaban ya tabbatar masa da cewa zai shiga tsakanin shi da gwamnan domin ganin sun samu daidaito.

Rikicina da El-rufai: Abun da shugaba Buhari ya fada mun - Shehu Sani

Rikicina da El-rufai: Abun da shugaba Buhari ya fada mun - Shehu Sani

KU KARANTA: "Kalar mutane 5 da suke jin haushin Buhari"

Legit.ng dai ta samu cewa Sanatan dai wanda yayi fice wajen sukar wasu daga cikin manufofin gwamnatin shugaba Buhari da ma na gwamnan na sa anyi ta mamakin yadda babu sunan sa a cikin jerin sunayen Sanatocin da suka canza sheka a farkon satin nan.

A wani labarin kuma, Jami'an hukumar nan dake yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC a Najeriya ranar Alhamis sun gurfanar da wani mutum mai suna John Abebe dake zaman suruki ga tsohon shugaban kasar Najeriya Olusegun Obasanjo a kotu.

Mista John Abebe wanda kani ne ga marigayiya tsohuwar matar Cif Obasanjo, Stella Obasanjo din EFCC ta ce ta gurfanar da shi ne a kotun bisa zargin sa da suke yi da anfani da takardun bogi wajen neman aikin hakar mai daga Najeriya din.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel