Ba zan iya aiki tare da Saraki ba – Shugaban PDP a Kwara

Ba zan iya aiki tare da Saraki ba – Shugaban PDP a Kwara

Shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Kwara Akogun Iyiola Oyedepo ya bayyana a ranar Alhamis, 26 ga watan Yuli cewa ba zai iya aikitare da wadanda suka sauya sheka daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) karkashin jagorancin Bukola Saraki ba.

Ya ce hakazalika sauran jami’an kwamitin ja’iyyar a Kwara ba za su iya aiki da wadanda suka sauya sheka ba.

Sanatoci biyu, Shaaba Lafiagi (Kwara ta arewa) and Rafiu Ibrahim (Kwara ta kudu) da wasu mambobin majalisar wakilai shida na daga cikin yan jihar da suka sauya sheka daga APC a ranar Talata.

Sannan ana sanya ran cewa Saraki da gwamnan jihar Kwara, AbdulFattah Ahmed, za su sauya sheka kwanan nan.

Ba zan iya aiki tare da Saraki ba – Shugaban PDP a Kwara

Ba zan iya aiki tare da Saraki ba – Shugaban PDP a Kwara

Oyedepo wadda yayi Magana a wani shirin radio a Ilorin, yace shugaban jam’iyyar PDP na kasa ya kafa kwamiti da zatayi shiga tsakanin kungiyarsa da masu sauya sheka.

KU KARANTA KUMA: Dalilin da ya sa na halarci taron sanatocin APC da shugaba Buhari – Shehu Sani

A halin da ake ciki bayan kiraye-kiraye daga masu ruwa da tsaki a jihar Kwara, gwamnan jihar, Dr Abdulfatah Ahmed ya yi Karin haske cewa yana iya barin jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Gwamnan ya bayyana cewa jam’iyyar bata kai yadda mutanen jihar Kwara suka zata ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel