EFCC ta biyo ta kan kanin matar Obasanjo

EFCC ta biyo ta kan kanin matar Obasanjo

- Yaki da cin hanci da rashawa ba sani ba sabo

EFCC ta gurfanar da sirikin tsohun shugaban kasar nan a kotu

- Har ma alkali ya sa a tura shi gidan maza ya fara karbar gabza

Wata babbar kotun tarayya mai zamanta a jihar Legas ta ingiza keyar wani babban dan kasuwa mai suna John Abebe zuwa gidan yari na Ikoyi kafin ta saurari korafin neman bayar da shi beli daga lauyansa.

EFCC ta biyo ta kan kanin matar Obasanjo

EFCC ta biyo ta kan kanin matar Obasanjo

John Abebe wanda ya kasance kani ne ga marigayya Stella Obasanjo tsohuwar matar shugaban kasa Obasanjo, ya tsinci kansa ne a gaban kotun bisa zarginsa da laifin damfara.

Tun farko dai hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzkin kasa zagon kasa (EFCC) ce ta gurfanar da shi bisa tuhumar aikata laifuka shida dake da alaka da damfara.

KU KARANTA: Hayaniya ta kaure yayin da kwamishinoni ‘Yan sanda 2 su ka bayyana don maye gurbin Kwamishina

EFCC dai ta ce tana zarginsa ne da kitsa zaren wata harkyalla a wata wasikar da ya rubuta daga kamfanin BP Exploration Nigeria Limited mai dauke da kwanan watan ranar 30 ga watan Nuwamba 1995 zuwa Inducon (Nigeria) Limited.

EFCC ta biyo ta kan kanin matar Obasanjo

EFCC ta biyo ta kan kanin matar Obasanjo

Kana kuma hukumar na zarginsa da yunkurin gujewa kamawa ta hanyar shigar da kara yana mai kalubalantar zargin da EFCC ke masa ta hanyar shigar da kara a kotu, hukumar ta bayyana lamba fayal din karar da ya shigar da ‘FHC/L/CS/224/2010’.

Sannan hukumar ta EFCC na sake zarginsa da yunkurin yaudarar kotun ta hanyar gabatar da shaidar karya, wanda hakan ya saba da sashi na 120(2) na kundin manyan laifuka ta Cap C17 na jihar Legas na shekara ta 2003 kamar yadda lauyan EFCC Rotimi Oyedepo ya shaidawa kotun.

Amma sai dai wanda ake karar ya musanta zargin, wanda hakan ta sanya mai shari’a Mojisola Dada ta saita masa hanyar zuwa kurkuku, sannan ta dage karar domin bawa lauyansa Uche Nwokedi (SAN) damar shigar da neman karbar belin wanda yake karewa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel