Almundahana: Shugabannin tsaro da Gwamnoni na yashe N241bn cikin asusun Gwamnati a duk shekara

Almundahana: Shugabannin tsaro da Gwamnoni na yashe N241bn cikin asusun Gwamnati a duk shekara

A ranar Larabar da ta gabata ne Cibiyar tabbatar da gaskiya ta duniya watau Transparency International ta bayyana yadda shugabannin tsaro da gwamnoni a kasar nan ke wawushe Naira Biliyan 241 a duk shekara.

Kamar yadda shafin jaridar Daily Trust ya ruwaito, shugabannin na tsaro da gwamnoni na aiwatar da zambar su ne tare da yaudara wajen karkatar da akalar dukiyar gwamnati ta hanyar wawushe kudaden gwamnati da aka yi tanadin su domin gudanar da harkokin tsaro.

Ƙungiyar mai hana yiwa tattalin arziki zagon kasa ta fahimci cewa, shugabannin tsaro da gwamnonin jihohi na karkatar da akalar kudaden da aka yi tanadin domin gudanar da harkokin tsaro dale janyo rashi da kuma barazanar sa a sassa daban-daban na kasar nan.

Almundahana: Shugabannin tsaro da Gwamnoni na yashe N241bn cikin asusun Gwamnati a duk shekara

Almundahana: Shugabannin tsaro da Gwamnoni na yashe N241bn cikin asusun Gwamnati a duk shekara

Mista Adeolu Kilanko, na Ƙungiyar ta Transparency International ne ya bayyana hakan yayin gabatar da wata lacca a birnin Ibadan dangane da yadda harkokin tsaro suka baiwa rashawa wurin zama a kasar nan.

KARANTA KUMA: Tsohon Gwamna Yuguda ya yi kira kan fatattakar jam'iyyar APC daga jihar Bauchi

Mista Kilanko ya yi kira ga Majalisar tarayya akan ta shiga ta fita domin tsarkake wannan barazana dake fuskantar kasar nan tare da kawo ma ta zagon kasar.

Legit.ng ta fahimci cewa, cikin shawarwarin sa Mista Kilanko ya nemi Majalisar ta sanya idanun lura tare da bibiyar diddigin shige da ficen duk wata dukiya da gwamnatin tarayya za ta tanada domin gudanar da harkokin tsaro.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel