Garkuwa da Dino Melaye: Ba mu da masaniya a kai – Hukumar Yan Sanda

Garkuwa da Dino Melaye: Ba mu da masaniya a kai – Hukumar Yan Sanda

Hukumar yan sandan Najeriya, shiyar babbar birnin tarayya Abuja, ta ce ba tada masaniya game da labarin cewa anyi garkuwa da Sanata mai wakilatan jihar Kogi ta yamma, Dino Melaye.

Labari ya bayyana cewa an yi garkuwa da sanata Dino Melaye da safiyar yau Alhamis, 26 ga wtaan Yuli a unguwar Gwagwalada yayinda ya nufi zuwa jihar Kogi domin halartan zaman kotu.

Sanata Ben Murray Bruce ta shafin sada zumuntarsa yace: “ Dan uwan Dino Melaye, Moses Melaye, ya sanar da ni yanzu cewa wasu yan bindiga cikin wata mota kirar Toyota Sienna sun tare motarsu kuma sunyi garkuwa da Dino Melaye.”

Garkuwa da Dino Melaye: Ba mu da masaniya a kai – Hukumar Yan Sanda

Garkuwa da Dino Melaye: Ba mu da masaniya a kai – Hukumar Yan Sanda

Amma hukumar yan sandan Najeriya ta musanta samun wannan labara inda tace babu wanda ya sanar da ita.

Kakakin hukumar, Anjuguri Mamza, ya bayyana hakan ga jaridar Daily Sun ne a wata hirar wayan tarho.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sunyi awon gaba da Dino Melaye

Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa kotu ta sammaci Sanata Dino Melaye ya bayyana a gabanta a yau Alhamis a jihar Kogi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel