Zurarewar $21: Majalisa ta gayyaci Baru, Kachikwu da shugabanin wasu hukumomi 2

Zurarewar $21: Majalisa ta gayyaci Baru, Kachikwu da shugabanin wasu hukumomi 2

- Majalisar wakilai ta gayyaci karamin ministan man fetur, Ibe Kachikwu, da sauran shugabanin kamfanonin man fetur

- Kwamitin na bincike ne a kan kudi $21 biliyan da ya salwanta sakamakon basusuka da haraji da aka dauki lokaci mai tsawo ba'a biya

- Kwamitin na sa ran gano matsalolin da suka janyo salwantar kudaden da dalilin da yasa ba'a dauki matakan da suka dace ba

A yau Alhamis ne kwamitin majalisar wakilai dake bincike kan bashin $21 biliyan da Najeriya ke bin kamfanonin man fetur na kasashen waje suka gayyaci karamin ministan albarkatun man fetur, Ibe Kachikwu da dukkan shugabanin kamfanonin man fetur dake Najeriya.

Ciyaman din kwamitin, Daniel Reyenieju (PDP, Warri) ya bayar da bayyani kan ayyukan kwamitin inda ya nuna damuwarsa kan yadda sauran hukumomin da nauyin karbo bashin ya rataya a kansu ke tafiyar hawainiya a kan batun.

Zurarewar $21: Majalisa ta gayyaci Baru, Kachikwu da shugabanin wasu hukumomi 2

Zurarewar $21: Majalisa ta gayyaci Baru, Kachikwu da shugabanin wasu hukumomi 2

KU KARANTA: Ba zan taba tsoma hannu cikin makircin tsige Saraki ba - Shehu Sani

Ya yi bayyanin cewa an daura wa kwamitinsa na musamman nauyin binciken kan matsayar majalisar na ranar Alhamis 18 ga watan Janairu da ranar 25 ga watan Janairun shekarar 2018.

"Kwamitin zata bincike ayyukan cinikayyar a kayi tsakanin kamfanin man fetur a kasar domin gano yadda akayi $12 biliyan ya salwanta, da kuma gano abinda yasa ba'a dauki matakan da suka dace ba wajen magance matsalar da kuma karbo bashi da harajin da suka salwanta.

Hakan yasa kwamitin da bukaci karamin ministan albarkatun man fetur din ya gabatar mata dukkan takardun cinikayyar da a kayi tsakanin hukumar man fetur na kasa da kamfanonin man fetur na kasashen waje.

Kwamitin na sa ran bita kan cinikayyar da a kayi da kuma yarjejeniyar da ke tsakanin hukumar man fetur na Najeriya da kamfanonin kasashen wajen da nufin gano matsalolin da suka janyo salwantar kudaden da haraji.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel