Canjin sheka: Sanatoci dake goyon bayan Saraki sunyi caa a kan Sanata Abdullahi Adamu

Canjin sheka: Sanatoci dake goyon bayan Saraki sunyi caa a kan Sanata Abdullahi Adamu

- Sanata Danbaba da Hama Misau sunyi wa Sanata Adamu Abdullahi kaca-kace game da wata labari da aka ruwaito wai ya fadi game da sanatocin da suka sauya sheka

- Sanatocin biyu sunce Abdullahi yana yadda irin wannan jita-jitar ne saboda ya neman alfarma daga fadar shugaban kasa bisa binciken da EFCC ke masa

- Sanatocin sun shawarci Sanata Abdullahi ya mutunta shekarunsa ya dena yadda irin wannan kalaman da ka iya tayar da zaune tsaye

Sanata Abdulahi Danbaba daga jihar Sakkwato da Sanata Isa Hama Missau daga jihar Bauchi sunyi tir da kalaman da aka danganta da Sanata Adamu Abdullahi na jihar Nasarawa inda aka ruwaito yace shugaban majalisa, Bukola Saraki, ya tattaro sunayen sanatocin da ya ke tunanin basu jin dadin abubuwan dake faruwa a APC ya kuma bayyana cewa sun fice daga jam'iyyar.

Canjin sheka: Sanatoci dake goyon bayan Saraki sunyi caa a kan Sanata Abdullahi Adamu

Canjin sheka: Sanatoci dake goyon bayan Saraki sunyi caa a kan Sanata Abdullahi Adamu

A sakon dake dauke da san hannun sanatocin biyu, sun gargadi Abdullahi cewa 'yan Najeriya suna da hankali saboda haka sun san cewa abu yadda za'ayi Saraki ya karanto sunayensu a matsayin wadanda suka fice daga APC alhalin suna zaune a majalisar ba tare da sun musanta hakan ba.

DUBA WANNAN: Ba zan taba tsoma hannu cikin makircin tsige Saraki ba - Shehu Sani

Sanarwan ta cigaba da cewa, "mutane irin su Adamu basu da aikin yi zai tayar da zaune tsaye da raba kawunnan al'umma. Wannan fa shine Sanatan dake yiwa Saraki biyaya sau da kafa a farkon kafa majalisar don yana neman kujerar Ciyaman din kwamiti amma daga baya ya rikide ya zama dan koran fadar shugaban kasa saboda yana tsoron laifukan da ya aikata a baya. Kowa yan san hukumar EFCC tana bicikensa da 'ya'yansa.

"Ba zai taba yiwuwa wani ya bayar da sanarwan sauya jam'iyya ba face ya samu amincewar 'dan majalisar dake son canja shekar. Muna son mu tabbatar masa cewa 'yan majalisa da dama zasu fice daga APC su bar Sanata Abdullahi Adamu ya cigaba da yadda jita-jitarsa.

"Sanata Adamu kawai yana kokarin tsirar da kansa ne amma ya kamata ya tabbatar cewa dukkan abinda zai fadi gaskiya ne. A matsayinsa na dattijo, ya dace ya kauracewa yadda labarai marasa tushe."

Sanatocin kuma sun karyata zancen a kace ya furta na cewa sanatocin jihar Kwara ne kawai suka koma PDP, Sanatocin sun lissafo sunayen 'yan majalisa daga wasu johohin da suka fice daga APC.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel