Tsohon Gwamna Yuguda ya yi kira kan fatattakar jam'iyyar APC daga jihar Bauchi

Tsohon Gwamna Yuguda ya yi kira kan fatattakar jam'iyyar APC daga jihar Bauchi

Tsohon gwamnan jihar Bauchi, Mallam Isa Yuguda, ya yi kira ga al'umma kan fatattakar gwamnatin jam'iyyar APC daga jihar domin samun dama ta kawo karshen cuzguni da wahalhalu da suke fama a halin yanzu.

A ranar Larabar da ta gabata ne Yuguda ya bayyana hakan jim kadan bayan karbar tuta ta jam'iyyar GPN (Green Party of Nigeria) a matsayin dan takarar ta na kujerar Sanata ta mazabar jihar Bauchi ta Kudu.

Kamar yadda shafin jaridar Today Nigeria ya bayyana, za a gudanar da zaben fitar da dan takara a ranar 11 ga watan Agusta.

Tsohon gwamnan wanda shine dan takara daya tilo na jam'iyyar sa ya bayyana cewa, tagayyarar al'ummar tare da wahalar cuzguni da suke fuskanta karkashin gwamnatin APC ya kai makura da ya kamata su kawar da ita.

Tsohon Gwamna Yuguda ya yi kira kan fatattakar jam'iyyar APC daga jihar Bauchi

Tsohon Gwamna Yuguda ya yi kira kan fatattakar jam'iyyar APC daga jihar Bauchi

Yuguda ya tabbatar wa da mazaban sa irin ingataccen wakilci da jakadanci da zai aiwatar a majalisar tarayya muddin ya samu nasarar lashe zabe.

KARANTA KUMA: Abinda ya sanya Hukumar 'yan sanda ta bukaci na gabatar da kaina - Saraki

Tsohon gwamnan ya kara da cewa, rawar da ya taka kan kujerar sa ta gwamna har a karo biyu cikin jihar ya tabbatar da nagarta da aminci na shugabancin sa.

A sanadiyar haka ne ya nemi al'ummar mazabar sa wajen yin cincirindo tare da gudanar da dandazo wajen kada kuri'u ga jam'iyyar sa ta GPN.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel