Jam'iyyar APC ta bukaci mabiyanta da kada su tada hankulan su

Jam'iyyar APC ta bukaci mabiyanta da kada su tada hankulan su

A ranar Alhamis dinnan ne jam'iyyar APC ta hori 'yayan jam'iyyar da kada su tsorata da barin jam'iyyar da wasu daga cikin mambobin jam'iyyar keyi

Jam'iyyar APC ta bukaci mabiyanta da kada su tada hankulan su

Jam'iyyar APC ta bukaci mabiyanta da kada su tada hankulan su

A ranar Alhamis dinnan ne jam'iyyar APC ta hori 'yayan jam'iyyar da kada su tsorata da barin jam'iyyar da wasu daga cikin mambobin jam'iyyar keyi. Cewa barin su jam'iyyar bazai shafi jam'iyyar da komai ba a zaben 2019 mai karatowa.

Idan zamu tuna a ranar 25 ga watan Yulin nan ne, 'yan majalisar wakilai 37 da Sanatoci 14 suka canza sheka daga jam'iyyar APC zuwa jam'iyyar PDP da ADC.

DUBA WANNAN: Wata duniya zata sakko kusa da tamu ranar 31 ga wannan watan - NASA

A wani jawabi da yayi wa manema labarai, mai magana da yawun jam'iyyar APC, Mista Ayoola Lawal ya kara tabbatar da cewa su dai suna nan a cikin jam'iyyar APC ba gudu, ba ja da baya.

Yace wannan lokacin ba na nuna tsoro bane, lokaci ne na kara tabbatar da goyon baya ga mulkin jam'iyyar.

"Tabbas babu jam'iyyar da take son rasa mabiyanta, ballantana wadanda suke kan mulki.

"Domin gujewa tantama, wannan damar su ce da damokaradiyya ta basu, don haka babu wanda ya isa ya hana su kuma dole ne dokar mu ta karesu" inji kungiyar APC Diaspora

Muna kuma kara jinjiina ga shugaban jam'iyyar mu, Adams Oshiomhole game da kokarin da yake wa jam'iyyar mu da kuma kokarin da gwamnatin mu take yi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel